BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 001


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA

      Fitowa Na (001)

Yadda Samari Suke Kawo Kayan Lefe Da Sadakin Su ah Wajen Budurwa, Su Rinjayi Budurwa Da Sunan ai Yanzu Kin Zama Matar Shi Domin Ya Kawo Komai, Saboda Haka Sai Budurwa Ta Bada Kanta Saurayi Ya yi Jima'i Da ita. Daga nan kuma idan ba'a yi Sa'a ba sai ya Gudu ya bar su da Sadakin da Kayan, Domin Ya Samu abinda yake so Shi. Toh Zina kuka yi, Domin Baki Zama Matar Ba Tukun, Koda ya kawo wadannan abubuwan Dukka, Ku biyo mu Cikin Rubun Mu. 

Shi Aure Ba Ya 'Daurewa Sai Da Waliyyi Da Sadaki Da Kuma Shaidu Biyu Adalai, idan Shaidun Ba Su Shaida a Wajen 'Daurin Auren Ba, toh ba Zai taba Saduwa Da Matar Ba Har Sai Sun Shaida Tukuna, Sabanin Abinda Yake Faruwa ah Yanzu, Yan Uwana Samari Mu Gyara Rayuwar Mu, Kai Ka Kawo Kayan Lefe a Wajen Yarinya Ka Bada Sadakin Ka komai Ka Gama Yi, an Sa Muku Ranan Sai Shekara Mai Zuwa Ko Kuma Nan Da Wata uku Masu Zuwa, Kayi Ta Rudin Yarinya Cewa ai Yanzu ita Matar Ka Ce, Ka Yita Rinjayarta Har Ta Zo Ta Mika Ma Kanta Ka Sadu Da ita, kai Kana Ganin Kamar Matar ka Ne, toh Ka Tabbata Cewa Kayi Zina Ne Karara ko Shakka Babu, Domin Kafin ta Zama Matar ka Komai ma Kayi Da ita, sai abinda Muka Ambata a Sama ya Auku Kafin nan, nan ma idan da Shaidun za su Ce Su fa Ba su Shaida Ba, toh Bai Halatta Ka Sadu Da Ita Har Sai Shaidun nan Sun bada Shaidar Eh Sun Shaida Kafin nan take Zama Matar Ka, Duk inda ka so ka je kayi Jima'i ita, amma wai don ka Kawo Sadakin ka da Kayan Lefen ka, ba shi ne Yake Nuna Cewa Yanzu Matar Ka Ba Ce, har kai kana iya taba ko ina ah Jikinta waya ce ma haka Sunnah ya koyar, taba jikinta ma da Kake yi Haramun ne mai Girman Gaske, Shi Ma Zina Ne, domin Kala Kala ne, Farji shine yake Gaskatarwa, mu kiyaye Dokokin Allah Yan Uwana Samari.
             Mafi 'karancin Sadaki Shine Rubu'in (1/4) Na Dinare Ya Halatta Ga Uba Mahaifi Ya Aurar Da 'Yarsa Budurwa Ba Tare da Izininta ba, ko da Ba Ta Balaga, idan Ya Ga Dama Kuma Ya iya Neman Shawaranta. Toh Wannan Zamanin Abinda iyaye yakamata Suyi Kenan, idan tanada wanda take so kuma duk Wani Abinda Shari'a Yace an Tabbatar da Cewa wanda Take son yana tare da su, shikenan sai abi Zabin ta, idan kuma Sabanin Shari'a Ne, Ke Kuma Budurwa Sai Kiyi Hakuri ki Bi Umurnin Iyayen Matukar suma sun miki Zabin da Shari'a ya Yarda da shi, sai kiyi Hakuri kiyi abinda suka ce Domin bara su zaba miki abinda zai Cutar da ke ba. Amma kuma idan su ma ba suyi zabin abinda Shari'a yace ba kawai sun bi son Zuciyar su, toh nan kuma sai a sake chanja Zani, Saboda Haka Iyaye Yakamata Kuyi Gaggawan Aurar Da Diyar Ku Daga Lokacin Da Ta Bukaci Yin Auren, Idan Kun Ki Aurar Da Suna Karatu Zasuyi tukuna, toh Zakuyi ta Haifar Zinace Zinace ne kawai a bayan kasa, ke kina ganin kin bama 'Yarki Tarbiya nagari bara tayi Zina ba, ba ki sani ba Rana tsaka ta Hadu Shedanin Saurayi Sha'awa shi kuma daman a kusa yake, duk yadda zata yi dole sai tabi abinda wannan Namijin zai ce mata, Domin kun ce mata ba Yanzu zatayi Aure ba, yar ki nata Zina da Wani Kullum ke baki sani ba, ita kuma ta daina kawo muku labarin zata yi Aure tunda ta samu abinda take so, amma idan kun Aurar da su ah Lokacin su, su je in ma za su yi Makarantan su je wannan ita da Mijinta ku kin fita Hakkinta, 
             idan ba Uba Ne Mahaifi ba zai Aurar Diya ba, misali irin wanda aka bai wa Wasiyya ne ko wakili, to ba zai taba Aurar da Budurwa ba sai ta Balaga kuma ta yi Izini Izininta Shine ta yi shiru ah Lokacin da ake Tambayar ta kina son waye idan tana son shi kenan, Uba ko waninsa ba Za su Aurar da Bazawara ba sai da Yardata, kuma lallai ta yi izinin da magana, kenan ita zata kiyi Magana ne ah maimakon Shiru.
              Ba a Aurar da Mace Sai da izinin Waliyyanta ko kuma wani mai Cikakken Hankali daga cikin 'Yar'uwan ta Kamar wani Mutum daga cikin danginta ko Sarkin Gari. An yi Sabanin Ra'ayi Dangane da Matar da Take Mara Matsayi, Ko ta iya Shugabantar da wani Mutum Ajnabi, Wato Wanda ba Danginsu ba, a kan Aurenta. 
              Da na Ciki Shi ne Ya fi Uba Mahaifi Cancantar Waliccin Mace, Shi Kuma Uba Ya fi 'Dan'uwa, to daga nan Duk Wanda ya fi Kusanci da Ita daga 'Yan'uwa Asibai Shi Ya fi Cancantar Waliccinta, idan 'dan'uwa na Nesa ya Aurar da ita, toh yayi ya Halatta ga wanda aka bai wa Wasiyya Ya yi Wa Yaro Karami Namiji Aure wanda aka ba shi iko, Amma bai Halatta Gare Shi Ba shi iko, amma bai Halatta gare shi ya Aurar da Yarinya Karama ba har sai dai idan Ubanta ya Umurce shi da Aurar da ita. 

Dangin na Nesa Zawul-arham, Wato Marasa Gado, ba sa cikin Waliyyai a Aure, Waliyyan Aure su ne dangi na Kusa, Wato Asibai, Bai Halatta wani ya Nemi Aure a kan Neman wani 'dan'uwan sa Musulmi ba, kuma kada ya taya wani abin Shayarwa a kan Tayinsa ah wajen Budurwa da yake Nema kenan, 
            Wannan yana Haramta ne idan suka Karkata ga junan su suka kusa daidaitawa ah Tsakanin su, toh Haramun ne kai ka ta so kace yanzu kana son ta kuma kaima Auren ta zakayi, Sabanin zamanin mu na Yanzu. Auren Shigari Wato Auren Farji Da Farji, Bai Halatta Ba, Kamar Yadda ah Yanzu Wasu Matan Suke Yi, har Suna Cewa Su Namiji Baya Iya Biya Musu Bukatar Su Ta Wajen Jima'i Kamar Yadda Mace Yar Uwan Su Zata biya Musu Bukatar Su Kuma Su Gamsu, Subhanallahi, Da Auren Mutu'a, Shi Ma Bai Halatta ba, irin Wanda 'yan Shi'a Suke yi, Shi Ne a yi Aure Zuwa dan Wani Lokaci kayyadadde, 
                  Kamar Misalin ace ya Aure ki na Sati Biyu ko Uku ko wata 2,toh wannan kwanan kin na Cika Shikenan kin Rabu dashi, koda bai ce ya Sake ki ba. 

Haka nan Auren Cikin idda Shi ma bai Halatta ba, da Auren da aka daura shi a kan Garari ko a wajen daurin Auren ko dangane da Sadakin duk bai Halatta ba, kamar Misali wai kwana kin can an Daura Aure ah Facebook Kudin Sadaki da Kayan Lefe da Waliyan duk ah Facebook aka gama shi, Yanzu Aure Sunnah Na Allah Da Manzon Allah Shine Yadawo Kamar Wani Wasan Yara, Shiyasa Allah yaketa Jarraban mu da wasu Musifu wanda bamu can da su ba, domin abubuwan yanzu sai kara yawa suke yi, Kiyama Ya Kusato mu sai dogon Buri.
         Haka nan yin Sadiki da wani abu da bai Halatta a sayar da shi a Shari'a ba, to duk Auren da ya baci a Dalilin bacin Sadakinsa sai a Warware shi kafin Miji Ya Sadu Matar idan Kuma Ya Riga ya Sadu da Ita, to Auren ya Tabbata, sai a bayar da Sadakin da ya dace da Matsayin ta, kuma duk Auren da ya baci tun a wajen daura shi kuma aka warware shi bayan ya Sadu da Matar, to lallai ne a bayar da Sadakin da aka kayyade a Tsakanin su sai an bata wannan Sadakin, 
              Kuma Haramci yana afkuwa da irin wannan Auren kamar yadda yake afkuwa da Auren Sahihi, Wato ba zai Aure ta ba har sai bayan tayi wani Auren, toh amma irin wannan Auren baya Halatta wadda aka Saki uku ga wanda ya sake ta, kuma irin wannan ba ya katange Ma'aurata biyu, wato Namiji da Matar Suna nan a Matsayin Saurayi da Budurwa _________

Ku Biyo Mu Ah Fitowa Na Gaba In Allah Yakaimu. 

Daga Zauren Muslim Woman Mata Zallah 
WhatsApp Group. 

MUHAMMAD TUKUR JALINGO 
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Kai Tsaye Ta WhatsApp Number Namu Kamar Haka 
08164223447. 
This Group Is Only For Woman Please.
Post a Comment (0)