BANBANCIN SALLAR FARILLA DA TA NAFILA

_*Tambaya:*_

Assalamu Alaikum

Dan Allah malam mene ban ban vin sallar farilla dana nafila

Sannan malam dan Allah wai acikin sallah wanda akeyi a baiyanane kawai ake karan ta surrsh bayan fatiha sauran na buyan kuma baa yi??

Allah ya kara ilimi.

_*Amsa:*_

_*¹* Bambanci tsakanin sallar *Farilla* da na *Nafila* shi ne;_

_➖ Ita sallar *farilla* sallah ce da Allah (ﷻ) ya ke wajabtawa a kan bãwa, Wanda idan mutum ya bar ta da gan-gan za a iya azabtar da shi. Kuma mutum ba ya da za6i a kan ta, dole ne a yi yanda ta zo, wato mutum ba zai ce ze yi sallar asuba raka'a hudu ba, ko ya yi raka'a biyar a sallar Zuhr da gan-gan, mutum ba ya da ikon yin hakan, ko ya yi Allah ba zai amsa ba._

_➖ Ita kuwa sallar *Nafila* sallace da mutum ya ga damar yi a karan kansa don neman lada a wajen Ubangiji, wanda idan mutum bai yi ta ba baya da wani zunubi a wajen Allah. Kuma mutum na da za6in ya yi raka'o'in da ya so, imma biyu, hudu, shida ko Takwas, har zuwa iya adadin da ya tabbata Manzon Allah (ﷺ) ba ya karawa daga hakan._

_*²—* Kwarai kuwa, raka'o'in da ake yin karatu a bayyane kamar Isha'i, to a biyun farko za a karanta *Fatiha* da *Surah* amma a biyun karshe Fatiha kawai ake karantawa. Haka ake yi a duk sauran sallolin amma banda Subhi saboda ita raka'a biyu ne kuma duka a bayyane ake yi._

Wallahu a'lamu.

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_

_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_

Wassalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

1 Comments

Post a Comment