*Tasowar Ibnu Taimiyyah da Iliminsa*
Ibnu Taimiyyah ya tashi a gidan ilimi kamar yadda muka gani. Ya kammala hardar Alqur’ani a cikin quruciya. Sannan ya kula da sanin ilimoman Fiqihu da Hadisi da Tafsiri da Arabiyyah. Ya soma karantarwa da fatawa da rubuta littafai da tattaunawa da malamai Munazara tun bai wuce shekaru ashirin ba. Koda ya cika shekaru talatin an fara yi masa laqabin Mujtahidi kuma “Mai raya Sunnah”. Yana da matuqar wuya a iya sifaita baiwar da Allah ya yi wa Ibnu Taimiyyah ta fuskar ilimi. Masu ba da labarinsa na ganin kasawarsu wajen bayyana irin hikimomin da ke tattare da shi ta wannan haujin. An lisafta malaman da ya gurfana a gabansu don daukar karatu aka tarar sun zarce malamai dari biyu. Akwai kuma littafan da ya karanta su sau da yawa a wurare daban-daban kamar Musnad na Imamu Ahmad. Game da nasa littafai shi kuma, Ibnu Taimiyyah ya wallafa sama da littafai hamsin a fannona daban-daban na addini, banda qananan wallafe-wallafensa da aka tara cikin Majmu’ul Fatawa mai sifili talatin da bakwai. Ya ishi mai karatu misali abin al’ajabi cewa, duk da yake Ibnu Taimiyyah bai wallafa Tafsirin Alqur’ani ba, amma malamai daga bisani sun wallafa shi daga cikin littafansa. Ma’ana an tattara wuraren da ya yi sharhi akan ayoyin Alqur’ani daga cikin littafansa a tsakankanin maganganunsa da kafa hujjojinsa, sai ga shi an samu kusan kammalallen Tafsiri mai Mujalladi hudu. Mujaddadi Ibnu Taimiyyah Muna iya cewa, Allah gwanin sarki ya tashi Ibnu Taimiyyah ne a wani lokaci da buqatar irinsa ta yawaita. Don kuwa a wancan lokaci al’umma tana fama da matsaloli da rikitta da tashin hankula na ciki da na waje. Daga cikin gida musulmi na fama da rabuwar kai, da yawaitar qungiyoyi da yaduwar bidi’ah da raunin ilimin furu’a. Ga kuma lalacin da ya yadu a cikin jama’a da zaluncin sarakuna da kwadayin malamai. Tsibbace-tsibbace da bokanci da duba sun zama gama-gari a cikin al’umma. Daga waje kuma ‘yan mishan sun kai ma musulmi farmaki, ‘yan Shi’ah masu kiran kansu Fadimawa sun hada kai da su. Sannan ga Tattar sun shelanta mummunan fada da musulunci da musulmi a duk in da suke a wancan lokaci. Shaihun musulunci ya fuskanci duka wadannan matsaloli da nufin magance su. Ya kuma samu taimakon Allah matuqa a wajen cimma wannan gurin nasa. Ga shi kuma Allah ya ba shi makamai da ya wuyata a samu wanda ya yi tarayya da shi a dukansu. Mutum ne da aka sifaita shi da kaifin basira da qarfin qwaqwalwa, har wasu ma na ganin bai tava sanin abu ya manta da shi ba. Yana da qarfin tuna ayoyin Alqur’ani da nassosan hadissai da maganganun malamai na kowane fanni. Don haka ya kasance mai kaifin hujja wadda take yanke wuyan abokin gaba nan take. Ga shi kuma jarumi da ba ya tsoron ko-ta-kwana. Don haka ba ya da ja da baya ga abin da ya sa gaba. Sannan yana da kwarjini a idon jama’a da kyawawan dabi’u da suka dada soyar da shi ga mutane. Ga shi mutum mai kishin gaskiya da qoqarin yada ta. Hada da halinsa na gudun duniya da rashin kula da jin dadinta. Irin wannan malami Allah ya dora shi a kan kyakkyawar hanya irin ta Annabawa wane irin canji kake tsammanin al’umma ba za ta ci moriyarsa ba ta hanyarsa? Dan Taimiyyah nan take ya rurrusa aqidun da suka zame ma musulunci tsutsar goro ta hanyar rubuce-rubucensa da wa’azozansa da karantarwarsa. Ya kece raini a wajen wargaza aqidun Yahudawa da na ‘Yan mishan. Ya yi faxa da qungiyoyi mabiyan son zuciya irin mulhidai da zindiqai da ‘yan Shi’ah da waxanda suka wuce wuri a Sufanci. Ya yi kira ga koma ma littafin Allah da Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba tare da ta’assubanci ga wani mutum ko qungiya ko mazhaba ba. Sa’annan ya kira sarakuna da talakawa zuwa ga yaqar kafirai waxanda suka keta hurumin musulmi, musamman dai Tattar. Ya kuma fita ya yi yaqi a matsayin xaya daga cikin sojoji. Tare da haka kuma Ibnu Taimiyyah ya kafa wata makaranta da Allah ya yawaita almajiranta tun daga wancan zamani har zuwa yau, kuma tana ci gaba da bunqasa har a naxe qasa. Wannan makaranta tasa tana mutunta magabatan Sahabbai da Tabi’ai da waxanda suka biyo bayansu, da shugabannin mazhabobi, tana kuma la’akari da ra’ayoyansu da fatawoyinsu baki daya. Tana kuma rinjayar da nassi ingantacce idan ya zo daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kan maganar kowa kome darajarsa. Wannan makaranta dai tana da daruruwan littafai da dubaiban malamai a cikinta. Dukkaninsu suna jingina kansu ga Sunnah da biyar magabata ba ga shi Ibnu Taimiyyah din ba.