MARABA DA WATAN RAMADAN 3

*MARABA DA WATAN RAMADAN*

       { 3 }

 GANIN WATA DA HUKUNCE-
 HUKUNCENSA

Haqiqa ALLAH (SWT) ya sanya rana ta zama ma'auni ga bayinsa don su san lokutan wasu ibadodi kamar Sallah. To bayan haka kuma ya sanya Wata a matsayin alama ta sanin lokutan wasu ibadodi na bauta masa kamar Azumi da kuma Hajji.

•ALLAH (SWT) Yace:

Ma'ana: "Suna tambayarka game da jinjirin wata kace musu, an sanya su don mutane su San lokuta da kuma aikin Hajji" .

(Suratul Baqara aya ta 189)
• ALLAH (SWT) ya Sanya watanni guda 12 acikin shekara kamar Yadda Yace:

Ma'ana: "Haqiqa qididdigar watan ni a wurin ALLAH guda 12 ne acikin littafin ALLAH......" .

(Suratul Taubah aya ta 36)
• Kuma ALLAH (SWT)
daga cikin watanni 12 ya ke6ance wasu ibadodi na musamman da ake aikatawa acikinsu. Kamar yadda Yace:

Ma'ana: "shi aikin Hajji yana da watanni sanannu....." .

(Suratul Baqara aya ta 197)
• Kuma ALLAH (SWT)
ya fada game da Ramadan (Azumi)
cewa:

Ma'ana. "Watan Ramadana shine watan da aka sauqar da Alqur'a ni acikinsa domin shiriya ga mutane da hujjoji da shiriya da kuma rarrabewa tsakanin gaskiya da qarya saboda haka Kowa ya shaida anga wata daga cikin ku to ya azumce shi....." .

(Suratul Baqara aya ta 185)
BAYANIN GANIN WATA DAGA MANZON ALLAH (SAW) !!!

Haqiqa Annabi (SAW)
yayi mana bayani mai gamsarwa acikin Hadithai daban daban kamar haka:

• Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Abdullahi dan Umar (R.A) Yace:

Annabi (SAW) Yace:

"Wata kamar haka yake da kuma haka" wato yana nuni da yatsun tafin hannunshi biyu sau 3 yana nufin kwana 30. Sannan yace da kuma haka" yana nufin kwana 29.

Yana nufin wani lokaci Wata kwana 30 ne wani lokaci kuma kwana 29. Malaman Hadith sunyi muwafaqa akan ingancinsa.

• Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Abu Hurairata (R.A) Yace:

Annabi (SAW) Yace: " kuyi Azumi idan kunga wata kuma Ku ajiye Azumi kuyi sallah idan kunga wata, idan an kare muku ganin wata saboda wasu giragizai to sai Ku cika qirgar sha'aban kwana 30" .

ABUBUWA GUDA 2 DAKE TABBATAR DA WATAN RAMADAN !!!

1• Ganin jinjirin watan idan sama ta kasance tangaram ba abin sake hana a ganshi na giragizai ko qura da makamantansu.

2• cika qirgan sha'aban kwana 30 idan ba a samu ganin watan ba ranar 29, wannan yana daga cikin dalilin Hadith da ya gabata.

GAME DA GANIN WATA A WASU QASASHE !!!

Idan ganin wata ya tabbata ga wani yanki na wata qasa to ya wajaba sauran yankuna su dauki Azumi idan sanarwa tazo musu ta hanyar da zata wajabta musu daukar Azumi, ba' a lura da banbancin sa6anin mafitar wata.

Wannan shine ra'ayin Mazhabobi guda 3 wato:

Imam Abu-hanifa, Imam Maleek da Imam Ahmad.

Amma a wajen Imam Shafi'ee sun inganta wannan hukunci ga makusanta wannan gari kawai, idan akwai nisa tsakaninsu da inda aka ga Wata to kowace qasa zata yi aiki da ganin watanta.

JAN HANKALI GAME DA GANIN WATA !!!

Ganin Wata ba wani Girma bane ko daraja bare ace sai sheikh ko malam wane zasu fara ganin shi ko kuma sai qasa mai tsarki ta ganshi kafin wata qasa ta ganshi ba, ba haka abun yake ba.

Ana iya ganin wata a America ko Isra'eela amma Saudia basu Ganshi ba.

Kafiri yana iya ganin wata, musulmi bai Ganshi ba illa dai ba'a amsar shedun ganin wata saiga Musulmai Adilai kawai.

Domin a zamanin Annabi (SAW) an samu wani Baqauye yazo daga garinsu yacewa:

Manzon ALLAH (SAW)
sunga wata da zaran Manzon ALLAH (SAW)
ya gamsu da shaidarsa a matsayinsa na musulmi sai kawai Yace Bilal (R.A) ya bada sanarwar daukar Azumi ko kuma ajiye shi.

Saboda haka a kula musulunci Addini ne mai sauqi ga wanda ALLAH ya sauqaqewa.

ALLAH Ya taimake mu (Ameen)

Zamu chigaba da yardar Allah...

Faridah Bintu Salis
(Bintus-Sunnah)

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

Don kasancewa damu a shafin telegram sai a danna koren rubutu👇 (link) 

https://t.me/miftahul_ilmi

 →Ga masu sha'awar Shiga Zauren *MIFTAHUL ILMI* WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248

Post a Comment (0)