Ramadaniyyat 1442H [18]
Babbar Ni'imar Allah Ga Sahabban Annabi (ﷺ)
1. Allah (SWT) yana cewa:
(Ya ku wadanda suka yi imani, idan kuka bi wani bangare na wadanda aka ba wa Littafi, to za su mayar da ku kafirai bayan imaninku. Ta yaya kuma za ku kafirce, ga shi kuwa ana karanta muku ayoyin Allah, kuma Manzonsa yana tare da ku? Duk kuwa wanda ya riki Allah, to hakika an shiryar da shi tafarki madaidaici. Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi takawa ga Allah hakikanin takawa, kuma lalle kada ku mutu face kuna Musulmi. Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kada kuma ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah da Ya yi muku yayin da kuka zamo abokan gaban juna sai Ya hada tsakanin zukatanku, sai kuka zamo 'yan’uwan juna a sakamakon ni'imarsa, a da kuma kun kasance a kan gabar ramin wuta sai Ya tserar da ku daga gare ta. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa don ko kwa shiriya.) [Ali Imran: 100-103].
2. Wadannan ayoyi da wadanda suka zo bayansu ayoyi ne da suke magana a kan sahabban Annabi (ﷺ) da koyar da su yadda za su mu’amala da wadanda ba Musulmi ba, musamman Ahlul-Kitabi.
3. Kamar yadda aka sani a tarihi cewa, Larabawa kafin bayyanar Annabi (ﷺ) sun kasance a cikin yake-yake da fadace-fadace a junansu da rayuwa ta zalinci da fin karfi. Duk wata kabilar mai karfi za ta yi kokin murkushe mai rauni, ta kuma 'yan'yanta a matsayin bayi. Wannan kuma ya hada har da mutanen Madina har zuwa lokacin da Allah (() ya sa Annabi (ﷺ) ya yi hijira ya koma Madina, ta zama daular Musulunci ta farko.
4. A garin Madina akwai manyan kabilu guda biyu, watau kabilar Ausu da Khazraju, sannan a wuri guda kuma akwai kabilun Yahudawa da suka zo suka yi sansani a unguwannin Madina daban-daban, bayan yaki ya tarwatsa daga garuruwansu a Sham. Don haka aka samu kabilun Yahudawa uku a Madina wadanda suka hada da Banun Nadhir da Banu Kainuka’a da kuma Banu Kuraiza
5. Yahudawa sun zo Madina sun tarar da manya-manyan kabilunta biyu watau Ausu da Khazraju suna ta gwabza yaki a tsakaninsu, yakin da ki ci ya ki cinyewa tsawon shekara dari da ashirin (120).
6. Su kuma Yahudawa suka ci gaba da rura wutar wannan yakin, ba don komai ba sai don su kara samun kafuwa a garin Madina, su kuma kara mamaye tattalin arzikinsu, suka rika sayar wa kowane bangare makamai don su yaki junansu.
7. Haka suka ci gaba da zama har ta kai ga an yi wani yaki da ake kira Yaumu Bu’as wanda a wannan yaki ne aka kashe manya-manyan mutane na kowace kabila daga cikin kabilun nan guda biyu, har ya zamanto babu wani babba mai fada a ji da ya rage daga dukkan bangorin guda biyu na Ausu da Khazraju. Wannan ya kara ba wa yahudawa damar mike kafa su yi yadda suka ga dama a garin Madina da tafiyar da sha’anin rayuwa a cikinta yadda suke so.
8. To bayyyanar Musulunci da hijirar Annabi (ﷺ) zuwa Madina ya taimaka wurin samun saukin fitinar dake tsakanin wadannan kabilu guda biyu.
https://t.me/miftahul_ilmi