NAYI KITSON ZARE KUMA NAYI WANKAN TSARKI DASHI..



*NAYI KITSON ZARE KUMA NAYI WANKAN TSARKI DASHI..*

      *TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum
Nayi kitson zare kuma nayi wankan tsarki dashi Wai wanka na baiyi ba
.
         *AMSA*👇🏻

Wa'alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh

 wasu malamai suna ganin idan mace zatayi wankan tsarki bayan daukewar jinin haila to zata warware kanta sun kafa hujja da hadisin Ummi Salamah Allah ya kara mata yarda, amma kuma malamai da yawa suna ganin cewa ba wajibi bane madamar ita matar tana da amintuwa cewa wannan ruwan idan tazo gudanar da wanka zai ratsa kanta yadda akeso to ba wajibi bane akan ta cewa sai ta warware kitson kanta, amma dai idan wankan janaba ne ba sai mace ta warware kitson ta ba, amma cewa wankan ta baiyi ba wannan yana bukatar dalili akai don haka wanka yayi in shaa Allah.

 Allah ne mafi sani

(( ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ))
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)