SOYAYYAR JUNA


💞 SOYAYYAR JUNA 💞

Sahabi Abud Darda'i Allah ya kara masa yarda yana cewa:
"Meye matsalarku da baza ku so juna ba bayan ku yan uwane a addini, hakika babu abunda ya rarraba kawunanku face lalacewar sirrikanku (abunda kuka boye azukatanku), da kun hada zukatanku akan abu daya to lalle da kunso junanku, hakan bai kasance ba (kiyayyar dake tsakaninku) sai dan karancin imani dake zukatantu. Wallah da ace kuna da yaqini na gaskiya game da alkhairin lahira da sharrinta kamar yadda kuke dashi a game da wani abu na duniya da kun kasance kunfi neman lahirar akan duniya, tir da mutane irinku banda yan kadan daga cikinku, baku tabbatar da imanin da ake gane imani nagartacce ba dashi, dan haka mun barranta daga gare ku. 

Allah Ta'ala ka sanya mana son juna ka cire mana gaba da kiyayya da sauran cutukan zuciya. 

# Zaurenfisabilillah 

https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)