TAMBAYA TA 016


Assalamu alaikum. 
.

*Tambaya:*

Mallam wani bawan Allah anyi auransa asabat akayi jana ixarsa ranar lahadi darana,
    Shin matarsa nada takaba kobata dashi.?
.

*Amsa:*


Waalaiku mussalam 

Matar da mijinta ya mutu bayan daura aure be tare da ita ba lallai zata yi iddah kuma za ta ci gado kamar yadda sahabi Uqbah bn Amir ya tabbatar lokacin da Abdullahi bn mas'ud ya yi hukunci ga matar da mijinta ya mutu bayan daura aure be tare da ita ba ya ce "tana da cikakken sadaki ba ragi ba qari za ta ci gado za ta yi iddah," Uqbah ya ce haka manzon Allah ya yi hukunci a wata mata wadda ake ce ma *بروع بنت واشق* kamar yadda tirmizy ya rawaito a Hadisi 1145 cikin jami'i nasa.

Sabanin saki in an daura aure ya sake ta be tare ba ba za ta yi idda ba kamar yadda Allahu swt ya fada a Suratul Ahzaab cewa:
*"ياايها الذين ءامنوا إذا نكحتم المؤمنات ثم طلقتموهن من قبل أن تمسوهن فما لكم عليهن من عدة تعتدونها“*
سورة احزاب ٤٩

ولله اعلم.
.
*Barr. Ukashatu Abubakar Giwa.*

*🕌Islamic Post WhatsApp.*
Post a Comment (0)