*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//17📿*
*GINSHIQI NA SHA BIYAR*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
"ME YA CE?" BA WAI "WA YA CE?" BA
A duk lokacin da muka dauki cewa wane ba ya kuskure to mun dora shi a matsayin da Allah bai kai shi ba, Annabawan Allah da kake ji ko ba ka koma hadisai ba za ka ga irin qalu-balen da suka riqa fama da shi, a Qur'ani, ana gyara musu, bare jama'ar qarshen zamani, don haka duk lokacin da muke son mu yi hukunci a kan wata magana da aka furta to mu kalli abinda aka ce ba wanda ya fadi ba, don kar kallon da za mu yi wa mutum ya hana mu mu karbi gaskiyar da zai fadi, wannan ma akwai dalili, in muka koma ga hadisan Annabi SAW za mu taras da hujja qarara.
Wani hadisi da Buhari ya rawaito dangane da abinda Abu-Huraira yake gani a mafarki, abincin bude baki ne da Annabi SAW ya ba shi ya raba, sai shedan ya zo yana son ya kamfata, Abu-Huraira ya damqe shi, ya roqe shi kan ya sake shi don yana da tsananin buqatar abincin ga iyali da yawa, in ya tafi ba zai dawo ba, to in ya zo ga Annabi SAW ya gaya masa sai ya ce masa maqaryaci, a qarshe ba yan an yi haka sau uku sai shedan din ya ce zai ba shi wata addu'a ba yadda za a yi wani shedani ya zo masa cikin daren in ya karanta har gari ya waye, ya ce ya karanta ayatul kursiy, da Abu-Huraira ya zo ya gaya wa Annabi SAW sai Annabin ya gasgata maganar amma ya ce shedandin maqaryaci ne.
Duk da tsananin gabar dake tsakanin musulmi da shedan, da ya yi gaskiya Annabi SAW ya bayyana aibunsa amma ya gasgata maganarsa, wani sa'in mutumin qwarai kan tabka kuskure, kuma ya rasa yadda zai yi ya wanke kansa, mu idan muka dube shi da matsayinsa muka kau da kai kan abinda ya fada anan ba mu yi adalci ba, matakin da muka dauka kuskure ne, don in muka dauki hakan zai iya yuwuwa kuma ka ga wanda muka saba masa a fahimta misali mun dauki cewa dan bidi'a ne, in ya fadi daidai zai yi wahala mu karba, komai mun dauka a baibai kenan.
Shi ya sa kallon maganar ba wanda ya yi ta ba ya fi komai adalci da zama daidai, Shehi Muhammadul Amin Shanqidi yake fadi a muqaddimar Tafsirinsa na (Adwa'ul Bayan) "Mukan inganta abinda ya bayyana mana a matsayin ingantacce da hujja ne ba tare da cewa mu 'yan mazahaba kaza ne ba, don maganar muke kallo ba wanda ya yi ta ba, kowace magana za ka taras akwai daidai da kuskure sai dai maganarsa SAW, don haka maganar gaskiya gaskiya ce koda mafadinta ba kowa ba ne"
Ya ce "Ba ka ga sarauniyar Saba'i da take bauta wa rana ita da jama'arta a maimakon Allah lokacin da ta fadi gaskiya Suleiman AS ya gasgata ta ba? Kafurcinta a lokacin bai hana shi ya gasgata ta ba? (Adwa'ul Bayan 1/6) Shaukani yake cewa "Mujtahidi shi ne wanda bai kallon wa ya fadi magana? Yakan dubi me aka ce ne, in ya ga kamar zuciyarsa tana qoqarin finciko shi ya guje wa 'yan kadan don bin dandazon jama'a, wato ya bi masu matsayi da daraja sai ya dubi fadin farfajiyar ilimi kadai, ya gano cewa lallai har yanzun wannan bangarancin da son kansa yana tare da shi, kuma bai ba ilimi haqqinsa ba (Adabut talab p43).
Ibn Qayyim ya yi wa wani littafi na Abu-Isma'il Al-Harawiy sharhi wato (Manazilus Sa'irina baina Iyyaka Na'abudu wa Iyyaka Nasta'in), a ciki ya ga wani wuri da shi Harawi din ya yi kuskure, ya yi qoqarin gyara masa amma ya rasa yadda zai yi wa maganar wata fassara, ga shi kuma Harawin yana daya daga cikin wadanda suke yi wa mazhabar magabata ginshiqi, masamman game da maganar kadaita sifofin Allah SW, yana da maganganu masu kyau game da umurni da abu mai kyau da hani da mummunan aiki.
Duk da haka lokacin da ya kauce hanya sai da Ibn Qayyim din ya ce "Allah ka yi wa malamin muslunci kuma masoyimmu rahama, sai dai qaunarmu da gaskiya tana gaba da shi, Ibn Taimiya RL yana cewa: "Aikinsa ya fi nasa" kuma gaskiya ne, tarihinsa wurin umurni da abu mai kyau da hani da mummunan aiki da yaqar 'yan bidi'a abu ne da ba mai iya kau da shi, ya yi suna wurin taimakon Allah da manzonsa, sai dai Allah ba zai yarda a sanya masa tufar sabonsa ga mai gaskiya abin gasgatawa ba, wanda ba ya fadin abu kan son rai, a wannan babin dai ya yi kuskure a lafazance da ma ma'anar maganar (Madarijus Salikin 2/394), daganan ne Ibn Qayyim din ya ci gaba da fadin inda ya yi kuskuren.
Yadda magabata ke ma'amalla da wanda ya yi kuskure ko yake yi gaskiya ba ma yi, irin zafin da muke dauka sai ka ga malaman na gaske sam ba sa yi, su janyowa suke yi ba tunkudewa ba, a kan maganar hoto yadda 'yan uwa suka yi zafi malam Jafar RL ya yi bayani ya shiga aka dauki hoton ma da shi, dalibai kowa ya yi ta fadin albarkacin bakinsa ga shi yanzu dukkansu ban ga wanda ba ya dauka ba, ya ce "Za ku bari, mu ma mun yi zafin mun ajiye" wallahi ilai-kuwa, a jawo fandararre ne abin nema ba wai a dada tunkuda shi nesa ba.
Zamuci gaba insha Allah.
*Gabatarwa: Abulfawzhaan*
*follow my Facebook page*
https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp
