NASIHOHI MASU AMFANI


*NASIHOHI MASU AMFANI*

📝 Rubutawa: *Sheik Aminu Ibrahim Daurawa (Hafizahullah).*

1- KADA KAYI RIGIMA DA MUTUM UKU

-Mahaifi.

-Malami.
 
-Shugaba.

2- MUTUM UKU DA MUTANE BASA KAUNA.

-Mai kudi marowaci.
 
-Talaka mai girman kai.

-Mai neman rigima bashi da karfi. 

3- HALIN MANYA UKU NE.
 
-Yin afwa ga wanda ya zalunceka.

-KA bawa wanda ya hana ka.
 
-Sada zumunta ga wanda ya yanke maka.

4- KA DARAJA MUTANE UKU A DUNIYA.

1. Dattijo.
    
2. Malami.

3. Iyaye.
 
5- KA TAUSAYAWA MUTUM UKU.

1. Tsoho.
  
2. mace. 
   
3. Yaro karami.

6- KADA KA MANTA ABU UKU.

1. Mutunci 
  
2. addini. 
   
3. Mutuwa. 
   
7- KA TSAFTACE ABU UKU.

1. Jikinka.
     
2. Tufafinka.
 
3. Zuciyarka.
     
8- KADA KA DENA NEMAN ABU UKU.

1. Ilimi.
         
2. arziki.
    
3. Aljanna. 

9- ABU UKU SUNA KARA IMANI.

1- Tilawal Al-Qur'ani.

2- Kiyamul-laili.

3- Azkhar.

10- ZAKA FUSKANCI MATSALA A KABARINKA IDAN KA MUTU DA ABU UKU.

1- Hakkin Wani.

2- Dabi'ar Annamimanci.

3- Hassada.

11- ABUBUWA UKU SUNA KAUDA FUSHIN ALLAH AKAN BAWANSA:

1- Istigfari.

2- Tausayawa waninka.

3- Sadaka.

12- IDAN ALLAH YA BAKA ABU UKU TO KA GODEWA ALLAH: 

1- Lafiya.

2- Wadata.

3- Basira.

13- KADA KA YARDA KA AURI MACE MAI DABI'O'I GUDA UKU:

1- Mai yawan fushi.

2- Maras sirri.

3- Marar tsafta (Kazamiya).

14- KA YI KOKARI KA GINA RAYUWARKA AKAN ABU UKU:

1- Son Allah da Manzonsa.

2- Gaskiya da Rikon Amana.

3- Hakuri da Jarrabawa a Rayuwa.

15- ABUBUWA UKU KA ROKI ALLAH (S.W.T) YA TSARE KA DA AIKATA SU:

1- Yanke Zumunta.

2- Zagin Sahabbai.

3- Mutuwa da hakkin wani.

16- MUTANE UKU KADA KA SAURARI MAGANARSU:

1- Makaryaci.

2- Magulmaci.

3- Malami mai kwadayi da son zuciya.

17- MUTUM UKU KADA KA YARDA SU DINGA KUSANTARKA:

1- Munafiki.

2- Mazinaci.

3- Maras kunya.

18- ABUBUWA UKU BA A SON JINKIRTA SU IDAN LOKACIN SU YA ZO:

1- Sallah.

2- Aure.

3- Jana'iza.

19- ABUBUWA UKU RIKO DA SU YANA SAMAR DA RABO A LAHIRA:

1- Kokarin ibada.

2- Kula da Nafila.

3- Amfani da Halal a Rayuwa.

20- ABUBUWA UKU SUNA HANA MUTUM TANADIN LAHIRA:

1- Dogon Buri.

2- Rashin karanta Alkur'ani.

3- Nisantar sauraron Wa'azi.

20- MUTANE UKU SUNA SAMUN TAIMAKON ALLAH:

1- Mutumin da yake Neman aure Don ya kare mutuncin kansa.

2- Mutumin da ya tafi jihadi, Domin daukaka kalmar Allah.

3- Bawa wanda aka dora masa fansar kansa.

21- ABUBUWA UKU NASA ZUCIYA TA GURBACE:

1- Rashin yarda da kaddara.

2- Aibata bayin Allah na kwarai.

3- Wulakanta Iyaye.

Allah Yasa Mu Dace.
Post a Comment (0)