*INA CIKIN SALLAR ASUBA, SAI NA TUNA BAN YI ISHA BA?*
*Tambaya:*
Salam Malam, mutum na cikin jam'in sallar Asuba, Ana raka'a ta biyu sai ya tuna bai yi sallar Isha'i ta daren daya gabata ba, zai yanke sallar ne yayi Isha'i, sannan ya sake Asuba ? ko zai cigaba da Asuba bayan an idar ya rama wacce ta gabata?
*Amsa:*
Wa'alaikum assalam, Idan mutum yana sallah sai ya tuna bai yi wacce take kafinta ba,to sallar da yake ciki ta baci, kamar yadda malaman Fiqhu suka fada, don haka ya wajaba ka yanke asubar, ka yi Isha, sannan ka dawo ka ka sake sallar Asuba.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
12/05/2016
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
