_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(14)
*ZAKKAR MA’ADANAI DA AJIYAR MUTAN DA:*
Abin da ake nufi da ma’adanai su ne, abubuwan da Allah ya halitta a cikin Kasa masu kima.
Ma’adanai iri uku ne: (1) Masu tsauri, wadanda suke sarrafuwa da wuta.
Kamar Zinariya (gold), azurfa (silber) da baKin Karfe da tagulla da darma da sauransu.
(2) Masu tsauri wadanda ba sa sarrafuwa da wuta. Kamar su, yaKutu da kwalli da farar wuta.
(3) Narkakku, kamar su fetir da kwalta, da gas da sauransu.
Malamai sun yi sabani dangane da nau’in ma’adanai da Zakka ke wajaba a kansu.
A fahintar Imamu Malik da Imamus- Shafi’i da Mazhabar Zahiriyya,
Zakka ba ta wajaba a kan ma’adanai sai idan Zinariya ce ko Azurfa.
A fahintar Imam Ahmad kuwa, za a fitar da Zakka daga duk abin da ake fitarwa daga Kasa, matuKar yana da Kima,
saboda fadin Allah (SWT).
(Duba Zakatul Ma’adini Na Mukhtar bin Umara Al-Husaini As-Shanidi sh: na 47.)
"يايها الذين آمنوا أنفقوا من طيبات ما كسبتم ومما أخرجنا لكم من الأرض".
“Ya ku wadanda suka yi imani, ku bayar daga tsarkakan abin da kuka noma, haka nan daga abin da Muka fitar muku daga Kasa”.
Shi kuwa Imamu Abu Hanifa cewa ya yi za a fitar da Zakkar ne daga ma’adanan da suke sarrafuwa da wuta.
_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*
Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_
*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi
Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
