WAƘAR FYAƊE


WAƘAR FYAƊE 

Bismillahi sarkina da babu mai taɓa masa ikonsa 
Salatinka a wajen manzo Aminu harda sahabbansa 
Baban Fati da babu wani manzo bayansa
Masu yin fyaɗe a gareku nake kira ku bar yinsa
Bashi da wata riba sai asara da a cikinsa
Ita rayuwa kowa na da ikon yin nasa.

Menene yasa ku ke cutar da 'yar uwata? 
Shin menene yasa ku ke cutar da ƙanwata?
Menene yasa ku ke cutar da yayata?
Shin menene yasa ku ke cutar da 'yata?
Wai shin menene ya sa ku ke fyaɗe wa mata?
Lallai dabbanci ya tabbata ga duk mai fyaɗe ga mata.

Ku sani matan nan fa su ba haja ce ba
Kuma matan nan su ba wasu kaya ne ba
Su matan nan ba litattafa ne ba
Su ma fa mutane ne ko baku gane ba?
Su ma fa suna da rai shin wai ko ba hakane ba?
To me yasa za ku tauye mu su abin da ba su tauye wa kowa ba?

Shi mai fyaɗe yafi kama da jaki a gani na
Ga shi da ƙarfi kuma ba wayo a tunanina
Ba nazari babu tunani sai halin ɓauna
Shi yasa ko da yaushe nakan kira shi sauna
Bashi da amfani sai dai isar da ɓarna
A duk sanda na ganshi nakan ji zuciyata na ƙuna.

Mai yin fyaɗe ka tuba ka daina ɓarna
Ka ji tsoron rabbbana Mahaliccina
Ka tuna da ranar tsayuwa a cikin rana
Ranar da za ka yi nadama bisa kan ɓarna
Da ka aikata yau a cikin rana
Wallahi ranar ba sauƙi ga duk wani mai ɓarna.

Rabbana ubangiji ka kare ɗiyanmu
Sarkina ubangiji ka kare ahalinmu
Ya Mannanu ka tsare duk 'yan uwanmu
Al'alimu kai ne masanin lamuranmu
Ka yaye mana musifar ga ta same mu
Ka shiryar da mu da duk al'ummar mu.


•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Twitter: @jamiluwriter 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Instagram: Jamiluwriter 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Facebook:
https://m.facebook.com/JamiluWriter/
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Tumblr: Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Bakandamiya: Jamilu Abdurrahman 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Telegram: https://t.me/Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
LinkedIn: https://www.linkedin.com/in/jamilu-abdurrahman-36b882118
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Haimanraees@gmail.com
──────⊹⊱✫⊰⊹────── 
Post a Comment (0)