NASIHAR SHEHU INYASS

★________________________________★
 NASIHAR SHEHU IBRAHIM INYASS
      (R•T•A) ZUWA GAREMU 'YAN
                       #TIJJANIYYA!"
★________________________________★

"KU YI HAQURI Tijjanawa!!!" Inji Maulammu Shehu Ibrahim Inyass Al-Kaulakhy (R•T•A).

ALLAHU AKBAR!

Kaji Shehu Ibrahim (R•T•A) Yana ba mu ha'kuri mu Ahlu 'Darikatit -Tijjaniyyah, dangane da Muzgunawa da Izaya ta Munkirai da suke yi mana.

Ga baitukan kamar haka:

1-ﺗﻼﻣﺬﺓ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﻟﺘﺠﺎﻧﻲ ﻓﺎﺻﺒﺮﻭﺍ **
   ﻋﻠﻰ ﻛﻴﺪ ﺃﻋﺪﺍﺀ ﻣﺪﻯ ﺍﻟﺪﻫﺮ ﺗﻨﺼﺮﻭﺍ .

2- ﻓﻤﺎ ﺿﺮﻛﻢ ﺟﻬﻞ ﺍﻟﺠﻬﻮﻝ ﻭﻗﻮﻟﻪ **
     ﻭﻟﻮ ﻓﺴّﻘﻮﺍ ﺃﻭ ﺑﺪﻋﻮﺍ ﺛﻢ ﻛﻔﺮﻭﺍ .

3- ﻓﻼ ﻳﺤﺰﻧﻦ ﺍﻟﺪﻫﺮ ﻗﻠﺒﺎ ﻣﻘﺎﻟﻬﻢ **
     ﻭﻟﻮ ﺃﻭﻋﺪﻭﺍ ﻓﺎﻷﻣﺮ ﻟﻠﻪ ﻓﺎﺻﺒﺮﻭﺍ .

4- ﺳﻮﺍﻩ ﺿﻌﻴﻒ ﻋﺎﺟﺰ ﻏﻴﺮ ﻗﺎﺩﺭ **
    ﻭﻟﻮ ﺟﻞّ ﻗﺪﺭﺍ ﻓﺎﻹﻟﻪ ﺍﻟﻤﻘﺪﺭ.

5- ﻭﻋﺎﻗﺒﺔ ﻣﺤﻤﻮﺩﺓ ﻻ ﻳﻨﻴﻠﻬﺎ **
    ﺳﻮﻯ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﺘﻘﻮﻯ ﺧﻔﻮﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﺻﺒﺮﻭﺍ .

6- ﻓﻌﺮﻭﺓ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺮﺵ ﻭﺛﻘﻰ ﻭﺇﻧﻨﺎ **
     ﺑﻬﺎ ﻣﻤﺴﻜﻮﻥ ﺍﻟﺪﻫﺮ ﻓﺰﺗﻢ ﺃﻻ ﺍﺷﻜﺮﻭﺍ .

7- ﺃﺭﺍﻛﻢ ﻣﻠﻮﻙ ﺍﻷﺭﺽ ﻻﺷﻚ ﻓﺎﺯﻫﺪﻭﺍ **
     ﻓﺪﻧﻴﺎ ﻛﺄﺣﻼﻡ ﺍﻟﻤﻨﺎﻡ ﺗﺒﺼﺮﻭﺍ .

8- ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺑﺘﻬﺬﻳﺐ ﺍﻟﻨﻔﻮﺱ ﻭﺃﻋﺮﺿﻮﺍ **
     ﻋﻦ ﺍﻟﻠﻐﻮ ﺣﺘﻢ ﺃﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﺍﻟﻤﻘﺪﺭ .

9- ﻟﻨﺎ ﺃﺳﻮﺓ ﺣﺴﻨﺎﺀ ﻓﻲ ﺧﻴﺮ ﻣﺮﺳﻞ **
     ﻋﻠﻴﻪ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎﺩﺍﻡ ﻳﻨﺼﺮ .

MA'ANAR BAITUKAN:
••••••••••••••••••••••••••••

1- Ya ku mabiya Shehu Tijjani, ku yi haquri da makircin maqiya, za ku samu Taimakon Ubangiji a kansu a kowanne Zamani.

2- Jahilcin jahili ko maganarsa, ba za ta cutar daku ba, koda kuwa suna daukarku a matsayin fasiqai ko 'yan Bidi'a ko Kafirai.

3- Kada maganarsu ta bata muku rai kwata-kwata, koda sun nana muku cewa zasu cutar da ku, domin duk lamari na Allah ne.

4- Duk wanda ba Allah ba kuwa rarrauna ne, gajiyayye, kuma bashi daiko akan komai, koda kuwa Alqadarinsa ya girmama domin Allah kadai Shine Mai iko akan komai.

5- ku sani cewa ba abinda ke sawa a samu kyakkyawan karshe sai ayyuka na tsoron Allah, don haka ku ji tsoron Allah kuma ku zamo masu haquri.

6- Lallai Igiyar Ubangijin al-Arshi mai karfi ce, Amintacciya, mu kuwa da ita muke riko, don kun rabauta ya kamata ku godewa Allah.

7- Ni ina ganin kamar ma kun zama jagorori a bayan kasa babu kokonto, to ku guji Duniya, domin Duniya kamar mafarkin mai bacci ce! Ku lura sosai.

8- Na umarce ku da tsarkake rayukanku, sannan ku kauda kanku daga duk wani zancen banza don babu makawa abinda Allah Yayi nufin Ya faru sai ya faru!

9- Kusani cewa mu da fiyayyen Manzanni (Manzon Allah S•A•W) muke koyi, Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, mutukar Allah nata taimakon bayinsa.

MADALLAH DA WANNAN MAI NASIHA, JAGORA NAGARI, WATAU SHEIKH ALHAJI IBRAHIM INYASS AL-KAULAKHY (R•T•A)!!!

Mun Gode Shehu!!!!
....
Post a Comment (0)