Ina mai rokon matan Aure, Zaurawa , yanmata da duk wata mace da ta iya karatu ta Taimaka ta karanta har karshe dan kuwa zai Amfane ki.
WAYE MIJI*
Salamu alaikum
Mata da yawa sun san ana cewa miji miji,kun san asalin kalmar?
Meyasa ake cemasa miji,does it make sense at all ace miji? Shi ba turanci ba ba larabci ba
The word miji ya samo asaline daga abinda hausawa ke cewa MIJIBINCIN LAMARI
Kunga ko daga sunan an nuna girmansa da kuma irin qimarsa
Miji komai lalacewar sa,komai talaucin sa,ko mai mugun halinsa sunansa mijinki indai da igiyar auransa a kanki
In har kina matsayin matarsa toh kuwa da haqqoqinsa akanki to dole sai kin sauke su,babu ruwan Allah da shi wane irin hali ne da shi me kyau ko mara kyau,in yana miki abinda bai dace ba wannan shi da Allah,amma ke fah dolen ki ki bishi kiyi masa biyayya a abinda bai sabawa Allah ba.
Kar ki yi gangancin cin zarafin mijinki ko yi masa maganganu marasa dadi dan wai shima yana yi miki,shi da yayi miki shi da Allah,ke kuma ladan hakurinkinna wurin Allah (me neman aljanna ina ruwansa da wani)
Ki cire a ranki cewa wai mutum kike wa biyayya,kisa a ranki Allah daya halicce ki shi kike yiwa,dan Allah ne yace kiyi aure kuma kibi mijinki shine hanyar aljannarki
Da yawa mata na making mistake wai suce su zasu qwatarwa kansu yanci da cin zarafin miji,da bijere masa da kin yi masa biyayya,to kin samu 'yanci kin rasa aljanna me kika yi kenan?
Ko kuma kaga mace tana cewa miji wai me ka ta bai mun? Toh wlh manzan Allah yace irin wannan matan ba zasu ji qanshin aljanna ba ma,haram ne mace tace miji ya sake ta ba tare da wani dalilie mai qarfi ba.
Babu wani dalili ko hujja da Allah zai karba daga wurinki duk randa kika tsaya a gabansa da laifin cin mutuncin miji,rashin biyayya,cin amanarsa da wulakanta shi
Miji yana da girman da sai da manzan Allah s.a.w yace da za'a umarci wani yayi wa wani sujjada toh da an umarci mace da tayi wa mijinta
Ku kalli fa,sujjadar da Allah kadai ake yiwa amma ace wai da za'a yi wa wani,ba'ace annabi ba,ba'a ce iyayenki ba,ba'a ce malaminki ba sai aka ce miji,kinga kuwa lallai ana so a nuna miki ne bayan Allah da manzonsa babu wanda ya chanchanci biyayyaa da total devotion irin mijinki
Mijinki yafi iyayenki,haka addinin musulunci yace,amma da an fada nasan zaka ga wasu suna kunfar baki,to ba haka mata masu ilimi suke ba
Daga randa akai miki aure iyayenki basu da wani katabus akanki sai abin da miji yace,girman da musulunci ya bawa miji ba kadan bane
Manzan Allah s.a.w yace da mace zata ringa yankar nononta tana gasawa tana bawa mijinta yana ci wlh da bata biyashi ba.
Kar ku ga ana ta zancen maza kullum basu da kirki basu da kaza basu da kaza,sunyi kaza sunyi kaza
Allah yana sane ya yi su a haka!
Ko an fada muku zaku samu aljanna a banza ne?
Hakurinku,da juriyarku Allah yake gwadawa,yana so yaga zaku yi masa biyayya akan abinda ya umarce ku
Amma mata basa ganewa,wata in ance tayiwa miji biyayya sai tace ay bashi da mutunci,yayi kaza yayi kaza
Wallahi duk hakurinki Allah yana kallo,kuma yana sane
Allah yace "inna ma yufassabireena ajreen bi ghairi hisaab"
Dukkan masu hakuri zasu shiga aljanna ba tare da hisabi ba
Me ya kai wannan dadi,ace duk zunubinki saboda kinyi hakuri zaki shiga aljanna bama tare da an bincika ki ba
Kuna shiga mala'i ku zasu tare ku suna muku oyoyo salamu alaikum bima sabartum,fani'ima uqbaddar!
Samun aljanna a bagas
In an mutu kenan ma
Kafin a mutu fah?
"Innallah ma'assabireen"
Allah yana tare da masu hakuri
Me ya kai wannan dadi,a cuce ki kiyi hakuri,wanda kika yi hakurin danshi kuma yace yana tare dake,in Allah yana tare dake yana kula da duk al'amuranki,yana cikin duk sha'aninki,yana kuma sane dake a komai
Me kike so bayan wannan
Allah yana sane da wanda zasu fara hakuri suce sun gaji,sai yace fasbir,kayi hakuri,sabaran jameela,hakuri kyakkyawa
Kunga kenan akwai hakurin da bai cika hakuri ba ko?
In kince hakurin ki ya qare kin dauki mataki toh me kenan kikayi? Wahalar da kikai a banza kenan ta tashi
Aljanna wani sai yayi yaqi an kashe shi zai samu,wani sai yayi shahada wani sai ya aiki na shekaru bila adadin,wani ma ba zai samu ba
Ke kuma sai aka ce miki aljanna tana qarqashin kafar mijinki
Da a ce miki je ki samo abu kaza a guri kaza da ace miki jeki samo kaza aduk inda zaki samu,it could be anywhere, kuma kafin ki dawo gida zai iya subucewa ya bata in har frm any where kika samo
Wanne zaki zaba? Ko wa zai ce zai je ya nemo a wurin da aka fada,komai wahalar daukar kuwa,tunda in ka dauka ka dauka kenan
Its not easy,Aljanna kike nema bayin allah suna zuwa suyi bautar shekara saba'in dan aljannar
Ke kuma fah?
In mijinki ya bata miki rai sai ki kalli ni'imar da allah yayi miki ta hanyar aure kafin ki fara nadamar aure,dan nadamar da yin wani hargagi ki wasu abubuwa da basu da ce ba yiwa Allah butulci ne
Komai ya same ki me dadi ko mara dadi ki godewa Allah
La'in shakartum la'azidanna kum,wa la in kafartum fa inna azabiy la shadeed
In kuka gode Min sai na qaramuku (ni'ima) in kuma kuka bijiremin/kafircemin(kuka qi gode min,kuka raina abunda nai muku)
Toh azabata me tsanani ce
Azabar Allah kika zaba ko biyayyar miji?
In kika duba ni'imar da rufun asirin da aure ya miki,tun daga ranar da aka daura aure an maida ke fa sabuwa kamar yau aka haife ki,an yaye miki zunubanki na baya da kika yi,saboda darajar aure
Kuma ko me kika yi a gidannan ladane,kiyi kwalliya lada,kiyi shara lada,kiyi girki lada,komai kika yi lada ne duk da amfanin kanki ne,in yaranki kike kula dasu lada ne
Allah yana sonmu yana so mu rabauta,komai ya tsara mana don dai mu tsira muji dadi
Amma me? Mata wlh sun bijirewa Allah ku fada min meyasa mata baza mufi yawa a wuta ba?
Komai Allah yayi manah mun bi son rai da zuciya mun watsar
Da kiyi sallah fah a masallaci gara kiyi sallah a dakinkin in akwai chan lungu a dakinma to yafi miki da kije wani wuri kiyi
Wai a nuna miki Allah ma yafi so ki bauta masa a cikin dakinki,dan ba inda yakai miki wannan dakin daraja.
Musulunci ya gatan ta mu,amma kuna bari maza muna bari maza suna mana wayo,suna mana rashin kirki muna ramawa muna biye musu,toh wlh biyu babu ne result din,kin zubar da kai a wurin miji kuma kije lahira kiji jiki,wa gari ya waya?
Rayuwar dai duk aljanna ake yi wa,ya zakai ka tsira? Dan nan dai ba shine madawwama ba,chan din shine gaskiya,to yaya zakiyi achan din ki samu guri me kyau? Abunda zaki kalla kenan
Kawai komai muyi tsakani da Allah,ba'a ce komai ki zauna a cuceki ba amma,there is a peacefull way to do everything
In kuma an cuceki din ko da kuwa ajalinki hakan yayi,baki fadi ba wlh
In kayi komai dan Allah wlh ko baka ga amfaninsa ba anan to ka jira babban rabo
Innallah la yukhliful mi'ad! Allah baya karya alqawari.
Tunda Yace zai yi zai yi,bazai barki ba.
Kar kice wai kina ta wahala amma shuru,kowa akwai irin yanda Allah ya tsara masa rayuwa,wasu anan zasu ji dadi,wasu achan,wasu kuma duka nan da chan din,kuma you can not question God yana da dalilin da yasa yayi hakan.
Mu tsaida imani,biyayyar miji acikin biyayyar Allah take,in kika ci mutuncin miji kema kin san wa kika yi wa
Dan idan babanki ya kawo me gadi yace ki bishi,ki yi mai biyayya in kin wulakanta me gadin nan hakan na nuna raina babanki kika yi kuma kin nuna bai isa ba
To uba ma kenan balle Allah da baza iya kwatanta shi da wannan abubuwan ba
Mu kiyaye iyakokin Allah! Dan wlh Allah abin tsoro ne ko ba dan wutarsa ba, Allah tun a duniya ba yadda ba zai yi da mutum ba.na tabbatar kowa tana da misalai.
Anan zamu tsaya Allah ya kaimu wani satin sai mu daura daga nan,har yanzu akan girman mijin fah muke,yet bamu ce komai ba..................
🖋📚Bilqeeau Abdullahi Al'ameen(mar'atussaliha)