DANCING FOR MY HUSBAND 1


*_MUNA CIKIN WANI ZAMANI WANDA ALFASHA DA YAÆŠA TA BA WANI ABU BANE A WAJEN MU!!! 0️⃣1️⃣_*


ببسم الله الرحمن الرحيم. 


_✍️ Sabuwar Shegantakar *“Dancing 4 Husbands Challenge A Social Media's"*_


إنا لله وإنا إليه راجعون!!!😔


Musulmai, idan muka kalli irin rayuwar da muke yi a yanzu zamu ga ta sha bambam da ta baya saboda fitintinu sun mana yawa, mune cikin yawan yaƙe-yaƙe, kashe-kashe, tsanantawa a wajen rayuwa, da kuma rashin adalci na shuwagabanni, tsadar rayuwa, tashe tashe hankula, kidnapping, fashi, sata, rashin albarka acikin rayuwa da makamantansu wanda hakan yay ta haifar da tambayoyi da yawa daga wajen mutane kan cewa: *_Mai Ya Kawo Wannan Musifun? Musamman mu anan arewacin Nigeria?_*

*Mai muka yi muka cancanci wannan? Ina muka dosa ne acikin rayuwar nan? Kuma mene ne za mu yi don hana faruwar wannan alamura?*

Yayin da masu hankalin cikinmu suka zurfafa tunani da tantance shin muna yin rayuwarmu ne ta fuskar bin maganar Allah - (Alqur’ani) - da kuma abin da Annabi (ï·º) ya umurce mu? amsoshin tambayoyin a bayyane suke cewa: *Mafi Yawanmu muna rayuwa ne a yanzu ta hanyar sanya Alkurani da Sunnar Manzon Allah (ï·º) a gefe guda. Mun bar Alqurani har ya fara Æ™ura, na cikin wayar mu da na'urar mu kuma har sun gaji suyi deleting din kansu ma. Sunnar Manzon Allah kallonta muke wata abace wacce bin ta sai yan kauye da wanda basu waye ba, don har kunya muke ji wajen nunata a cikin halayenmu da rayuwarmu ma baki daya!*


Sai gashi kullum wasu fitintinun ne suke kuma bullowa wanda kwanan nan akayi ta yaki da masu *_Pre Weeding Pictures_* sai gashi wata sabuwa ta fito kuma mafi muni da batanci wanda ana neman tsokano Allah ne *_matan aure da mazajensu suna rawa wasu ma da iyalansu suna video suna dorawa duniya ta gani, wasu ma tsirara suke da kayan bacci, wasu suna rungume juna, wasu ma lalacin abin acikin dakin bacci akan gadonsu_* إنا لله وإنا إليه راجعون 🤦‍♂️ Malam Ina Muke Son Zuwa Ne? 

Irin wannan rayuwar da muke yi ko dabbobi basa yi wallahi, to amma babban dalilin faruwar hakan shine Barin Allah da mukayi da kuma koyarwa ta Abul Qasim (ï·º). Shiyasa babban malamin nan masani *_Shamsudden Muhammad Abi Bakar Ibn Qayyim Jauziyyah_* yake cewa:

*_Duniya ta girgiza, Sammai sunyi duhu, musifa ta bayyana akan Æ™asa da teku saboda muguntar mugaye, da masu aikata mugunta. Albarkatu sun shuÉ—e, kyawawan ayyuka sun ragu, rayuwa ta Æ™azantu saboda muguntar azzalumai. Hasken safe da duhun dare suna zubar da hawaye, saboda munanan ayyukan da ake yi a doran Æ™asa. Malaman marubuta daga cikin mala’iku da wasu daga cikinsu sun koka ga Ubangijinsu saboda yawan barna da girman zalunci da yayi yawa a Æ™asa._*

Me yasa muka kai zuwa ga irin wannan yanayin?🤔 Ga abin da ya malam ya faɗa a gaba don bayyana wannan sabon abu:

*_Lokacin da aka watsar da Alƙur'ani mai girma, da Sunnah, saboda ana tsammanin basu isa ba ga rayuwar dan adam, kuma idan aka nemi ra'ayin mutane, misalai, hankali, da kalmomin (sauran waɗanda ake kira) malamai, an lalata halayen mutane, lalatattun mutane suka cika. Zuciyoyinsu sukayi duhu, fahimtarsu ta rikice, kuma hankalinsu ya dagula._*

*_📓AL-FAWA’ID: – na ibn Al-Qayyim_*
Post a Comment (0)