TALLAR LAXMMI BOMB TA KAFA TARIHI
Izuwa yanzu dai duk inda ka duba a shafukan yanar gizo babu labarin da ya fi jan hankali a harkar fina-finan Indiya sama da sabuwar tallar shirin jarumi Akshay Kumar da ta fita a jiya juma'a mai suna Laxmmi Bomb. Tarihi ya kafu, kuma mutane sun sha mamaki cikin kofuna bayan tallar ta haΙa jimillar makallata miliyan saba'in (70 Million Views) a cikin awoyi ashirin da huΙu bayan fitar tallar. Hakan ya sa ta zama talla mafi kalluwa daga cikin tallolin fina-finan Indiya baki Ιaya. Sai dai abin tambayar shi ne? Wani saΖo wannan fim ke Ιauke da shi? Kuma menene 'yan kallo za su tsammata daga wannan fim? Ga wasu abubuwa da zan iya tsakurowa daga cikin tallar wannan shiri.
1. FIM ΖIN AKSHAY KUMAR NE: Wanda duk ya san wanene jarumi Akshay Kumar to baya buΖatar sai an yi masa dogon sharhi akan abinda jarumin zai iya yi a fim. Ko da yake wannan fim ya zo da wata sabuwar siga da ba a taΙa ganin jarumin a cikinta ba, babu shakka shirin na Ιauke da duk wani abu da masoyan jarumin ke so dangane da shi.
2. HAΖI NA MUSAMMAN: Wannan shiri shi ne fim na farko da jarumi Akshay Kumar zai fito tare da tsaleliyar kyakkywar jarumar nan mai tashe wato Kiara Advani. Hakan ya jawo hankalin mutane da dama duba da irin ganiyar nasara da kowannensu ke ciki a yanzu tare kuma da tunanin abin da zai ka iya fitowa daga gare su idan suka haΙu a fim tare. Kuma kamar yadda tallar ta nuna, haΙin zai bada citta har da masoro.
3. FIRGICI DA BAN TSORO: Fim Ιin Laxmmi Bomb fim ne na ban tsoro, don haka 'yan kallo sai su shirya. Domin kuwa mun gano jarumi Akshay Kumar yayin da fatalwar wata mace ta shiga cikinsa inda kafin ka ce kwabo ya canja daga mai barkwanci zuwa masheΖi.
4. NISHAΖI: Bisa ga dukkan alamu wannan shiri na Laxmmi Bomb ya shirya tsaf domin tabbatar wa da duniya laΖabin nan da aka kiran jarumi Akshay Kumar da shi wato Mr. Khiladi. Domin kuwa tallar Laxmmi Bomb ta nuna mana irin nishaΙin da za a samu a cikin shirin musamman ta fuskar barkwanci.
5. TARIN KODUMO: Duba da irin yadda wannan talla ta samu karΙuwa, na san ko ba a faΙa ba za ku iya fahimtar gamsarwar da ke cikinta. Akwai SuburbuΙa, calikanci, soyayya, waΖa mai daΙi, ban tsoro, madarar kafce da kuma sunΖi-sunΖin buhunan kodumo!
Tabbas alamu sun nuna za ta fashe sosai a bikin diwalin bana. Shin ko Akshay Kumar zai zama sabon sarkin Diwali da Laxmmi Bomb kamar yadda yanzu ya zama sabon sarkin Bollywood? Lokaci ne zai bamu wannan amsar.
©️✍π»
Jamilu Abdulrahaman
(Mr. Writer)
Haimanraees@gmail.com
π« *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* π«
