SHARHIN FIM ƊIN THERI


SHARHIN FIM ƊIN THERI 

Theri (ma'ana tartsatsi) fim ɗin Indiya ne da aka shirya shi cikin harshen Tamil kuma ya fita ne a cikin shekara ta 2016. Wannan fim ya yi matuƙar kyau kuma ya samu karɓuwa a wajen 'yan kallo. 

• Bada Umurni - Atlee

• Ɗaukar Nauyi - Kalaipuli S. Thanu

• Labari/Rubutawa - Atlee & S. Ramana Girivasan
(Dialogue)

• Sauti/Take - 
G. V. Prakash Kumar

• Horas Da 'Yan Wasa - 
George C. Williams

• Tacewa - Ruben

• Kamfanin Da Ya Shirya - 
V. Creations

• Kamfanin Da Ya Yaɗa - 
SPI Cinemas (Chennai)
Friday Film House (Kerala) 
Carnival Motion Pictures (Kerala)

• Ranar Fita - 14 April 2016

• Tsayin Shirin - mintuna 158 

• Ƙaaa - India

• Harshen Shiri - Tamil

• Kasafi - est. ₹75 crore

• Kasuwancin Box office
est. ₹160 crore

An fara ɗaukar wannan shiri ne a farkon watan Yulin 2015 a garin Chennai. An ɗauki sashen faɗace-faɗacen shirin ne a cikin watan Nuwambar wannan shekara, sai dai kuma an samu matsala a yayin ɗaukar sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi a garin na Chennai. Hallau dai, rashin yanayi mai kyau ya sa suka soke ɗaukar wani sashe na shirin a ƙasar sin su ka koma Bangkok. 

An saki wannan fim ne a ranar 14 ga watan Afrilun 2016. Haka kuma an fassara shirin zuwa harshen inda aka sa masa suna Policeodu. A ƙarshen kwanakinsa shida da fara haskawa a sinima, Theri ya kawo kuɗi kimanin ₹1 billion (US$14 million). A United Kingdom kuwa, ya karya tarihin da fim ɗin Enthiran (2010) ya kafa na box office collection for the first weekend. Vijay ya lashe gasar Entertainer of the Year da rawar da ya taka a shirin a bikin 6th South Indian International Movie Awards da aka yi a shekarar 2017

LABARIN SHIRIN 

Joseph Kuruvilla yana rayuwa ne cikin jin daɗi da nishaɗi a birnin Kerala tare da 'yarsa mai suna Niveditha wacce ake kira da Nivi. Yana kuma sana'a biredi tare da Rajendran. A haka dai har ƙaddarar rayuwa ta sa ya haɗu da Annie wacce ita kuma malama ce a makarantar su Nivi, har dai suka zama abokai. 
Bayan wasu faɗi tashi gami da tataburza tare da 'yan dabar yankin, Annie sai ta fahimci cewa Joseph ba kowa bane face marigayi Vijay Kumar. Joseph ya ba Annie labarinsa a matsayin Vijay, amma ya gargaɗeta da kada ta faɗa wa Nivvi. 

Shekaru biyar da suka gabata, Vijay Kumar nagartaccen ɗan sanda ne mai gaskiya da ya kai matsayin DCP a Chennai. Watarana sai ya karɓi kundin wani laifi na fyaɗe da kuma kisa da aka yi wa wata ɗalibar na'ura mai suna Raji. Binciken da yayi sai ya gano cewa ba kowa bane ya aikata wannan laifi Ashwin, ɗan gidan Labor Minister Vanamaamalai. Vijay sai ya kashe Ashwin kuma ya bayyana kansa a matsayin makashin wa Vanamaamalai wanda shi kuma ya sha alwashin ɗaukar fansa a kansa. Ana cikin haka ne kuma, sai Vijay ya faɗa soyayyar wata ɗalibar likitanci mai suna Mithra inda ba a jima ba suka yi aure jikin jin daɗin rayuwa. 

Sai dai kash! Jin daɗin su bai ɗore ba, domin kuwa Vanamaamalai, da ɗan uwansa Ratnam tare da 'yan dabarsu sun faɗo musu gida inda suka kashe Mithra da mahaifiyar Vijay. Sannan kuma sun jigata shi kansa Vijay ɗin matuƙa. Da har sun yi niyyar halaka jaririyarsu Nivvi, amma sai Mithra ta samu damar cetonta yayin da take gab da mutuwa. Mithra ta roƙi Vijay da ya kula mata da 'yarta a bayan ranta tare da tirsasa shi ya yi mata alƙawarin zai bar aikin ɗan sanda gaba ɗaya. Vijay sai ya yi ƙaryar ya mutu, ya canja sunansa zuwa Joseph Kuruvilla ya kuma koma Kerala tare da Nivvi tare da abokinsa kwanstabul Rajendran domin ya kare Nivi daga Vanamaamalai da 'yan dabarsa. 

Watarana, yayin da Nivi ta hau wata motar bas tare da sauran ɗalibai da nufin da nufin zuwa yawon buɗe ido, sai birkin motar ya karye motar ta faɗa ruwa da ƙyar da siɗin goshi dai Vijay da Annie da Rajendran tare da mutanen wurin suka ceto Nivi da sauran yaran. Daga baya sai Vijay ya gano cewa Vanamaamalai ne ya yi sanadiyar faruwar wannan hatsari da nufin ya kashe Nivi bayan ya gano suna raye. Hakan yasa Vijay ya harzuƙa kuma ya sha alwashin ajiye alƙawarin da ya ɗauka ya kashe Vanamaamalai kawai kowa ya huta. 

Daga nan sai Vijay ya fara aiki a matsayin fatalwar kansa inda ya fara yi wa yaran Vanamaamalai ɗauki ɗai-ɗai. Da fari dai ya kashe SipetaKarikalan wanda yana daga cikin yaran Vanamaamalai da aka je gidansa da su aka kashe Mithra. 'yan sanda sai suka ruɗe, domin an yi kisan ne a cikin ofishin kuma su duk tsammaninsu shi ne Vijay ya mutu. 

Daga nan fa sai mace-mace ya fara ƙaruwa inda Vijay ya hankaɗo Ratnam daga saman ginin da yake yi ya mutu. Daga nan kuma sai aka fara zargi Vanamaamalai saboda sun samu saɓani, hakan ya sa dole shima ya ɓoye. Daga ƙarshe dai sai Vijay ya bari yaran Vanamaamalai suka kama shi saboda ya shiga mafakarsa. Bayan ya kashe shi tare da yaran nasa sai ya sagale shi a sama ya bar wajen. Da 'yan sanda suka zo suka ga ba kowa sai gawawaki, sai hankali fa ya ƙara tashi.


Ashe kwamishinan 'yan Sandan Chennai wato Sibi Chakravarthi ya san cewa Vijay yana raye, kuma shi ne ma ya ɗauke shi aiki a asirce domin ya yaƙi ta'addanci, amma kuma sai ya fito ya ke bayyanawa duniya cewa Vijay fa ya mutu. 

Bayan wasu shekaru, sai Vijay, Nivi, Annie da Rajendran suka koma Ladakh inda Vijay ya canja suna zuwa Dharmeshwar. Amma ya ci gaba da aikinsa na kawar da ta'addanci a asirce. 


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Post a Comment (0)