*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
➖➖➖➖➖➖➖➖
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_*
_*Daga zauren*_
_*📌Albahral Ilmu🌴🌴*_
.
.
_*HUKUNCIN IDDAR MACE MAI SHAYARWA*_
:
_*Tambaya*_
:
Idan aka saki Mace tana Shayarwa yaya hukuncin Iddarta zai kasance idan Jinin-Al'ada yadena zuwa mata saboda Shayarwar da takeyi??
:
*_Amsa:_*
:
Wāto kamar yadda yake sanannen abu awajen Mutāne cewa akwai Nau'ikan-Mātā da yawa waɗanda Jinin-Al'āda yake tsayā musu alokacin da suke Shāyar da Jāriransu, wasu bazāsu sāke ganin Jiniba har sai sun yāye ''Ɗan'' da suke Shāyarwa, Saidai wasu Mātan jinin yakan dāwō musune bāyan Shekara ɗaya, wasu Mātan kuma bayan watanni Shidda(6) ko wani abu makamancin haka sai suga Jinin-Al'ādarsu yazo, yāyin da wasu Mātan kuma dāma kwata kwata su Jinin-Al'āda bāya tsaya musu sakamakon Shāyarwar da sukeyi, kawai da Jinin-Bīƙi yāɗauke musu sai kuma Jinin-Haila yabiyo bāyansa idan lokacin zuwansa yāyi,
:
To idan ya kasance Mace batayin Jinin-Al'ada sakamakon Shāyar da Jariri da takeyi, Mālamai sukace irin wannan Mātar idan aka Saketa to zātayi ta jirane har sai randa tayi Jini-3 koda kuwa hakan zai kaita zuwaga lokacin da zāta yaye Jaririn da take Shayarwar wato Shekaru biyu kenan, to dōlene har sai tagama waɗannan Jināne-Guda-3 sannan iddarta zāta ƙāre, danhaka kenan idan Sakine irin na "Kōmē" to Mijin yana da dāmar yace yādāwō da Mātarsa koda kuwa bāyan Shekara biyune da yin Sakin matuƙar dai batayi Jini-3 atsakāniba, wannan maganar kuma dukkan Mālamai-Fuƙahā'u sunyi Ijmā'i akan haka, Hujjarsu kuwa itace faɗin Aʟʟāн(ﷻ) dake cikin wannan āya:
:
''والمطلقات يتربصن بأنفسهن ثلاثة قروء'' (البقرة/228)
MA'ANA:
(Mātan da) aka Sakesu zāsu zaunane harsuyi Jini-3 (tsarki-3)
:
Danhaka kenan idan Mace tanāso Jinin yazo mata da wuri to saita bāyar da Jārīrin nata wata Mātar ta Shāyar dashi, kokuma tayi amfani da wani magani wanda zai janyo mata al'adarta alokacin datake Shāyarwar amma da Sharaɗin ya kasance ba Saki bane irin na "Kōmē" domin idan Sakine irin na "Kōmē" to bai halatta tayi amfāni da māgani dan ta janyo al'ādarta ba, domin kuwa Mijinta yana da haƙƙi akanta na ya mayar da ita kokuma yarabu da'ita, amma idan Sakine irin wanda ba Sakin-Kōmēba to ya halatta tasha maganin da zai janyo mata jinin da wuri, amma shima da Sharaɗin ya kasance anāda tabbas kokuma zato mafi rinjane akan cewa maganin yadace da Jikinta bazai cūtar da'itaba,
:
To amma idan ya kasance Al'ādar-Mace tāɗaukene sakamakon wani Sababi kamar irin na Shāyarwa kokuma rashin lāfiya, daga baya kuma sai wannan Sababin yagushe, Misāli ace tawarke daga rashin lāfiyar, ko ta yāye ''Ɗan'' da take Shāyarwa, amma duk dahaka jinin bai zomata ba, to anan sai mafi yawa daga cikin Mālamai sukace Iddar irin wannan Mātar zata zaunane har tsawon Shekara guda cur, wāto watanni-9 amatsayin mafi gālibin tsawon lokacin da mai ciki takeyi kafin ta haihu, Saikuma watanni-3 amatsayin Idda, idan anhaɗa yāzama watanni-12 kenan,
:
Danhaka idan yakasance Mace zatayi Iddāne na tsawon Shekara ɗaya, Misāli ace tayi watanni-11, kwatsam kawai sai taga Jinin-Al'āda yāzo mata, to yanzufa lissafincan da tayi na watanni-11 yariga yārūshe, danhaka yanzu dolene sai tā sāke jiran zuwan Jini na-2 da na-3 idan bai zoba har ta sākeyin wata Shekarar guda cur, to shikenan tāgama idda, amma idan taga Jini na-2 yazo koda kuwa tasakeyin wasu watanni-11 da zuwan na farko, to anan ma lissafinta yāsake rūshewa, danhaka dole sai tā sāke jiran wani Jini na-3 yazo sannan tagama idda, idan kuma jini na-3n bai zoba har tasakeyin wata Shekarar shikenan tagama Iddarta,
:
```(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)```
:
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_
*--------------------------*
*_•Ga mai sha'awar
* shiga Zauren
*📌Albahral Ilmu 🌴🌴*
_*ta whatsApp sai yayi cikakkiyar sallama tare da suna da Address nasa zuwa⬇ ga lambar mu*_
_*07064746551*_
〰〰〰〰〰〰〰〰〰