HABA SHEHI!


HABAAA SHEHI.!!!

Hakika mutanen arewacin Nigeria suna cikin rudani da tashin hankali na rashin tsaro wanda in ba addu'a ba, babu abinda ze fidda mu daga cikin wannan yanayi.

Ana cikin dar-dar na abinda ya faru a cikin kwanakin nan se aka samu wata mummunar magana daga babban malamin dariqan tijjaniyyah asheikh Dahiru Usman Bauchi (Hafizahullah).

Inda yai fira da yan jarida, ya nuna alhininsa bisa ga abinda yan uwansa fulani suke yi na bata sunan fulani a kasar har ta kai duk inda aka ga fulani yau a kasar nan ana jin haushin su.

 Shehi ya basu shawarwari masu kyau akan wannan abin da suke yi.

 Se a karshe dan jaridar yai ma shehi tambaya kamar haka.
"ALLAH YA KARA MAKA LAFIYA WANI SHAWARWARI ZAKA BA HUKUMOMI NA GWAMNATI A MATAKAI DABAN-DABAN. 

 Abinda mu muka sa rai shi ne shehi zeyi halin dattako ya fadi irin abinda yake ganin in gwamnati ta yi za a samu saukin lamura. Amma kashhhh! Se aka samu akasin haka. Ga amsar da shehi ya bayar: 
" INA JAWO HANKALI MUSAMMAN NA FULANI, KAR SU SAKE SHIGA WANI ABU WANDA YAKE KUSA DA KIDNAPPING DIN, INA JI MASU TSORO KAR SU KOMA SU ZAMA YAN IZALA, KAR YAN IZALA SU KWASHE SU SUCE ZASU YI MASU WANI ABU. YA ZAMO SUNA YAN FASHI KUMA SU KOMA SU ZAMA YAN IZALA. YA ZAMA SUN BAR ADDINI KENAN GABA DAYA...''

Wannan shine wani sashi na amsar wannan tambayar da aka yi wa shehi.

SE NACE:
Wannan ba ita ce amsar tambayar ba. Domin gwamnati aka ce ya ba shawara.

 A baya mun sha jin shehi yana kiran sunan uban mu Malam Abubakar Mahmud Gumi, karara yana cin mutuncin sa a guraren karatukan sa mabanbanta.
Wanda na ji na baya bayan nan shine wanda ya kira sunan malam Abubakar Mahmud gumi da dalibinsa Malam Sama'ila Idris yaci mutuncin su. Inda ya kira malam da "SAMA'ILA #IBLIS a maimakon sama'ila idris.

A hasashena dalilin da yasa shehi yin wannan maganar shi ne ganin yadda Dr Ahmad dan gidan malam Abubakar gumi yake shiga kauyuka yana tattaunawa da yan ta'adda. Shi ne hassadar sa ta motsa, domin a baya yayi da mahaifin Dr Ahmad . (Malam Abubakar gumi) yanzu malam ya kwanta ya mutu ya dawo da hassadar kan dansa.
Wanda wannan ABIN KUNYA NE.

ai in ka wuce wasan QASA to kayi na KUDI.
 (Hausa ce).

Abin mamaki kuma nidai har yanzu Allah be hada ni da inda naji malam abubakar gumi ya kira sunan shehi karara yaci mutuncinsa ba.

WANNAN SHI NE HALIN DATTAKU.

Sannan a tarihin musulunci babu wadanda sukai ma addinin annabi Muhammadu hidima kamar ahlus sunnah. 

An sha zagin annabi a kasar nan amma tsakaninku da Allah wasu malamai suka fi fitowa suyi raddi dan bada kariya ga annabi s.a.w.
(Tsakaninka da Allah ka amsa min. Da kai nake yi kai me karatu)

Duniyar musulunci da littafan sunnah take taqama.

 Amma duk da haka Hassada ta hana shehi fahimtar haka.


Sannan abin takaici se ga wasu mabiyansa suna kokarin kare wannan KASASSABAR da yayi. Saboda tsabar son zuciya.

Wallahi wallahi wallahi.
Ko da ace malam Abubakar gumi na raye yai irin wannan kasassabar se mun juya masa baya mun ankaraddashi kuskurensa, a irin wannan yanayi da muke ciki na tashin hankali.
Wanda ba abinda muke bukata kamar zaman lafiya

Dan haka in dai mutum ba son zuciya ta kamashi ba yasan wannan magana bata dace aji ta daga bakin
DATTIJO, MALAMI, MAHADDACI, JAGORAN WATA AL UMMAH irinsa ba.

KIRA:
A karshe kira na ze je ga ahlussunnah musamman yan qungiyar izala da kuyi hakuri kar wannan yasa ku zagi Shehi. Domin ko bakomai ai DATTIJO NE, kuma SA'AN UBAN MU NE.

Sedai muyi masa fatan karin lafiya da imani,
In mutuwa ta zo kuma Allah yasa ranar sa ta karshe ta zama mafi alkhairin ranar sa a duniya.

Abu Sadiq ke ma kowa fatan alkhairi da fatan samun dawwamammen tsaro a kasarmu Nigeria.

 Amin
Post a Comment (0)