MIJINA BA YA BIYAMIN BUƘATA


*MIJINA BA YA BIYA MIN BUKATA, MENENE SHAWARA?* 

https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN

                             *TAMBAYA* ❓

Assalamun alaikum, Malam mace ce mijinta ba ya iya biya mata bukata saboda raunin mazakutarsa, kuma ashe abin da ya raba shi da uwar gidansa kenan.

Kasancewar ba ya biya mata bukata ta shiga cikin halin damuwa, sannan ta yanke shawarar cewa: in ya kira ta shimfidarsa ta daina zuwa, to malam ta yi laifi game da wannan shawarar da ta yanke ?

                                  *AMSA* 👇

Wa alaikum assalam, A shawarata kamata yayi a kira magabatansu su xauna su tattauna a gano yadda xa'a warware matsalar.

Idan har ya tabbata ba cikakken namiji ba ne to xa'a bashi shekara daya ya nemo magani.

Idan ya warke shikenan, in bai warke ba kuma xa ta iya fadawa cikin haram idan taci gaba da xama dashi, to ya halarta a raba auran, kamar yadda aka raba da uwar gidan.

Yana daga cikin manyan manufofin aure: ma'aurata guda biyu su katange junansu daga haram, in har aka rasa wannan to akwai matsala a xamantakewar aure. 

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)