HUKUNCIN TAƁA JIKIN MACE


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D3VpiJzm6WECmizK6DEBfi



*HUKUNCIN TAƁA JIKIN MACE* 



*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum mln barka da Jumu'ah Allah ya amshi ibadummu Amin, tambayata itace Dun Allah mln mimene hukuncin mutun minta idan yazu wuren Wanda zai aura hiri yike taba jikenta kuma har hannu yakesa mata ariga har kissn din juna sukeyi, kuma shi yanada mata, dun Allah mln inaso ayi jan hankali sosai gamida wannan, na gode Allah yabada ikon amsawa🙏


*AMSA*👇


Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Lallai Allah madaukakin sarki idan ya haramta wani abu yakan haramta dukkan wata hanya komai kankantarta da zata kai zuwa ga aikata wannan abun. Saninmu ne tattaba ko shafar jikin mace babbar hanya ce wadda ke motsarda sha’awa zuwa ga aikata zina, kuma mun sani zina tana cikin zunubai guda bakwai wadanda suke da saurin hallakar da mutum. Bayan yin shirka da Allah sai kuma zina, saboda muninta Allah yace kada ma mu kusanceta. 

Lallai duk macen da ta bada kanta wa wani dan iska mayaudari wanda baya sonta baya son rayuwarta da tarihinta da sunan wai yana sonki ko kuma kunyi alkawarin aure wallahi duk yaudara ce kuma wallahi koda ya aure ki sai yaci mutuncinki ya sake ki, duk wanda zaki masa haka kina tunanin zai aminta cewa idan wani yazo gunki ba zaki bashi irin damar da kika bashi ba? Kiyi tunani da kyau yake ‘yar uwa!.Lallai irin wadannan matan sune ake kira da jakar gayu ko shaddar kasuwa domin kamar yanda kika bashi wannan damar da sunan soyayya idan wani wanda yafi shi iya zakin baki da yaudara yazo zaki amince masa, kuma har abada bazai taba amintuwa dake ba..Sannan ba wani sonki da yake kawai wani abu ya keso ya cimma akanki na mummunan aiki ya bata ki dajin kunyar duniya data lahira. Shi kuma ya tafi abunsa yayi aurensa. Kuma zai ce sai mace nar kafa. Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisidaga Abu Hurayrah 

Manzon Allah (saww) yace an rubuta ma kowacce ga’bar Dan Adam nata kason na zina:
Zinar hannu ita ce ta’bawa (ta’ba matar da bata halatta gareka ba)
Zinar Qafa shine tafiya (wajen da bai halatta gareka ba).
Idan idanu shine Kallo (kallon abinda bai halatta gareka ba).
Kuma hadisi ne Sahihi.
Don haka wannan abinda kakeyi shima zina ne. Kuma BABBU SHAKKA duk irin yadda kayi da ‘ya’yan mutane sai an aikata irin haka akan Qanwarka ko yayarka, ko UWARKA MAHAIFIYA, ko Qanwar Mahaifinka, ko Qanwar mahaifiyarka, ko kuma ‘YARKA TA CIKINKA.

Akwai wani Sarki daga cikin Sarakunan Daular ABBASIYYAH, yayi kokonton anya kuwa wannan maganar haka take?
Don haka ya sumbanci matar da ba tasa ba, kuma shima yana nan wata rana ya haifi ‘Ya mace, kuma ta girma ta zama budurwa, tana cikin tafiya a kasuwa, ga Dakaru masu kareta.
Amma duk da haka sai da wani ‘Dan-Dako yazo ya rungumeta ya sumbanceta.
Ya kai Saurayi!! Ina kiranka kaji tsoron Allah ka tuba, tuba irin wacce Allah yake so. Ba wai tuba irinta mayaudara ba.
Domin hakika babu alamar Nadama acikin maganganunka. Kuma Allah yana jinka.
Idan kana tunanin cewa zaka je kayi Iskanci da ‘ya’yan mutane, sannan zakaje kace ka tuba, don kar ayi da ‘Yarka, to kayi kuskure.
Allah ya fika wayo, kuma yana nan yana jiranka a madakata.
Idan ka tuba, tubar gaskia, in Allah yaga dama ya karba shikenan. In kuwa tuban muzuru kayi, to kaima kasan sakamakon mayaudara shine Tozarta anan duniya da kuma lahira.
Allah ya kiyaye mu daga aikata zina da dangoginta.
Post a Comment (0)