HUKUNCIN AUREN KASHE WUTA



اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎
Daga Zauren
 📌 *Albaharal Ilmu*🌴

✍🏻Rubutawa
    Abdulkadeer Umar Alshinkafawy.


*HUKUNCIN AUREN KASHE WUTA* 


*TAMBAYA*❓

MENENE HUKUNCIN AUREN WANDA YASAKI MATARSA SAKI UKU, SANNAN YASA WANI YA AURETA YA SAKETA DOMIN YASAKE AURENTA TA DAWO GIDANSA?
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﺍﻟﺴﻼﻡ ﻋﻠﻰ ﺃﺷﺮﺍﻑ ﺍﻟﺨﻠﻖ ﺍﻟﻠﻪ .


*AMSA*👇

Idan mutum yasaki matarsa saki uku, bazata sake zama halal agareshi ba harsai wani ya aureta, Aure na kwadayi bawai Auren kashe *wutaba,* Sannan suka rabu da ita, saboda fadin Allah madaukakin Sarki acikin *Suratul Baqara ayata (230)*
( Idan miji yasaki matarsa bazata sake zama halal agareshi ba, bayan yasaketa harsai ta auri wani mijin daban).
*Abu dauda yaruwaito hadisi (2076)* Annabi Sallallahu Aaihi wasallam ( ya tsinewa mai Auren kashe wuta, dawanda ya aura danta halatta gawanda yasaketa).
Albani Ya Ingantashi Acikin sahihu Sunan Abu dauda.
Haramunne da mijin farko suka hada baki banda sanin daya mijin, ko matar da mijinne suka hada baki banda sanin ita matar, Malamai Sunyi Sabani Amma ingantacciyar magana shine kota wacce hanya akayishi haramunne.
Shaikul Islam Ibnu taimiyyah yace:
" Hasan da Naka'iy sukace: idan daya daka cikin ukun yabada himma to Auren kashe wutane, mijin farko dana biyun da ita matar, An ruwaito haka daka Ibnul Musayyeeb, lafazin Ibrahimun naka'iy: idan niyyar daya daka cikin Su ukun ( Mijin farko, kona Biyu, ko matar) Auren kashe wutane, wannan nakarshen bataccene bazata halatta ga mijin farkon ba....
*Fatawa Kubra na Shaikul Islam ( 6/298)*
Domin Samun cikakkun bayanai akan hakan duba
*" Madalibu Ulin nahayi (5/127) da Al-Mugny " (7/139 " da " Kashshaaful Qina'i" (5/96) da " Hashiyatu Dasuqy " (2/258), Da I'lamul muwaqqe'iynah (4/36)*
Saboda haka wannan Aurene batacce kuma bata halatta ga mijinta nafarko ba, kuma kaba'irane cikin manyan zunubai.
Zata halatta agareshine kadai idan miji nabiyu abisa radin kansa yanemi Aurenta, harsai yadan-dani dadinta ta dan-dani dadinsa sunzauna sosai, randa Allah yakawo musu rabuwa suka rabu, idan mijin farko yaga haryau yanada Bukata akanta saiya aureta tadawo wajansa.
Wallahu A'alamu.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﻧﺸﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﻧﺘﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ .
Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
07064746551
 *_Group Admin: ▽_*
 *Abdulkadeer Umar*
Post a Comment (0)