NA AURI MATA BA TARE DA NA SAN TANA DA NAKASA BA, KUMA BA'A FADA MIN BA, YANZU NA JI BANA SON TA,YA ZAN YI?


NA AURI MATA BA TARE DA NA SAN TANA DA NAKASA BA, KUMA BA'A FADA MIN BA, YANZU NA JI BANA SON TA,YA ZAN YI?

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

*TAMBAYA*❓

Assalamu alekum
Akaramakallah inama fatan alkairi Akaramakallah ina neman mafitane ko nace shawara nayi Aure ne satin da ya wuce gaskiya tindaga ranar da aka kawota ban kusancetaba sai jiya na nemeta sai na tatar da nonanta guda dayane ma'ana nono daya take dashi dayan dan karami ne kamar nonon namiji ba komai awajen ma kuma gaskiya iyayenta basu fadamin tana da wannan matsalar ba kafin Aure Sheik wallahi yanzu naji bana kaunarta sede ban nunamataba na rasa miye yakemin dadi dan Allah Shek katemakamin da mafita me yakamata nayi

*AMSA*👇

Wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in. 

Subhanallahi. Jama'a musulmi wannan ha'inci ne kuma zalunci ne bai halasta ba. Babu boye aibi a harkar neman aure saboda guje ma irin haka. A batun neman aure shara'a ta halasta ka ambaci munin halin mutum ko aibin sa.

 قَالَتْ فَلَمَّا حَلَلْتُ ذَكَرْتُ لَهُ أَنَّ مُعَاوِيَةَ بْنَ أَبِي سُفْيَانَ وَأَبَا جَهْمٍ خَطَبَانِي فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((أَمَّا أَبُو جَهْمٍ فَلاَ يَضَعُ عَصَاهُ عَنْ عَاتِقِهِ وَأَمَّا مُعَاوِيَةُ فَصُعْلُوكٌ لاَ مَالَ لَهُ انْكِحِي أُسَامَةَ بْنَ زَيْدٍ)). 
قَالَتْ فَكَرِهْتُهُ ثُمَّ قَالَ: ((انْكِحِي أُسَامَةَ بْنَ زَيْدٍ)). فَنَكَحْتُهُ فَجَعَلَ اللَّهُ تَعَالَى فِيهِ خَيْرًا كَثِيرًا وَاغْتَبَطْتُ بِهِ. 

Haka ma shara'a ta haramta kallon mata ajanabiyyai, amma idan kana neman wata mace da aure, toh shara'a ta halasta ma kallon ta, duk don gudun je ka dawo. Annabi yace, idan dayan ku na neman wata mace da aure toh ya kalle ta idan ya samu dama

506 - 231 - «إذا خطب أحدكم المرأة فإن استطاع أن ينظر منها إلى ما يدعوه إلى نكاحها فليفعل» .
حسن. د ك هق عن جابر. الإرواء 1791. الصحيحة 99.

A wata riwaya kuwa umarni ya bayar, yace tafi ka kalle ta

859 - 416 - «اذهب فانظر إليها فإنه أحرى أن يؤدم بينكما» .
(صحيح) ... [حم قط ك هق] عن أنس [حم هـ قط طب هق] عن المغيرة بن شعبة. الصحيحة 96.

Bawan Allah kayi hakuri, waliyyan ta suka cuce ka, ifan sun sani, ko kuma ita ce ta ha'ince ka, idan tana da hankalin sanin ya kamata. Sannan baka da laifi don ka kyamace ta, hakan ya faru ne saboda ha'intar ka da aka yi. Domin da ace tun asali an fada maka, ka sani, kuma ka ci gaba, da a yau ba zaka kyamace ta ba.

Yanzu abu guda zaka yi, shine, idan zaka dauki hakan a matsayin jarrabawa shike nan, sai kayi hakurin zama da ita a haka, shi aka fi so, domin baka san abin da Allah ya taske ma na alkhairi a wurin ta ba. A sanadiyyar haka sai Allah ya azurta ka da mata masu nono biyu duniya da lahira, kamar yadda yace 

(... فَإِن كَرِهۡتُمُوهُنَّ فَعَسَىٰۤ أَن تَكۡرَهُوا۟ شَیۡـࣰٔا وَیَجۡعَلَ ٱللَّهُ فِیهِ خَیۡرࣰا كَثِیرࣰا)
[Surah An-Nisa' 19]

Ma'ana kilan kana da wata bukata da kake so wajen Allah kuma sai Allah ya saka sababin biyan bukatar na cikin zama da ita wannan matar ta ka. Idan ka rabu da ita, shike nan, ka kabar da bukatar ta ka. Allah ya nanata mana cewa sau tari alkhairi na cikin abin da ba ma so

(... وَعَسَىٰۤ أَن تَكۡرَهُوا۟ شَیۡـࣰٔا وَهُوَ خَیۡرࣱ لَّكُمۡۖ وَعَسَىٰۤ أَن تُحِبُّوا۟ شَیۡـࣰٔا وَهُوَ شَرࣱّ لَّكُمۡۚ وَٱللَّهُ یَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ)
[Surah Al-Baqarah 216]

Amma idan ba zaka iya zama da ita a haka ba, toh sai ka sake ta saki daya. Domin zama da wanda baka so ba zai yiyu ba, kuma ko da za'a tilasta maka, toh zata zauna cikin wulakanci da zalunci, don haka zama tsakanin ku zai wahala ko da ita tana son ka.

Amma ta ci sadakin ka duka saboda kwanciyar aure da ta ratsa tsakanin ku, sai dai kana da damar ka bi wanda ya ha'ince ka idan ka san shi domin amsar sadakin ka hannun sa.

Daga karshe ina mai bayar da shawara ka yi hakuri ka rufa mata asiri ka zauna da ita zama na tausayi da mutunci. Sannan ga samari, yan mata da iyayen su kuwa, su lazimci gaskiya da baiyana ta ga juna ba ma kamar ga wadanda zasu yi aure, ko da kuwa ciwon sickle cell ne.

Wallahu ta'ala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)