ƘANINA YANA CHATTING DA 'YAN MATA KUMA BA AUREN SU ZAI YI BA


*KANI NA YANA CHATTING DA "YAN MATA KUMA BA AUREN SU ZAI YI BA*

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum malam Ina da qani mu biyu iyayenmu suka rasu suka bari kuma dukkan mu munyi aure to amatsayina na yayarsa matar sa bata taba kawo mun qorafiba saboda macece da banason kai qarar mijinta Ako Ina to sai kwana ki tazo gidana take kika mun akan cewa yafara canza halayen chatting da yammata kuma ta tuntube shi da zancen sai yacema ta sai me aishi mijin Mace hudune.To nazaunar dashi kuma na tambaye shi ko yanada ra'ayin qara aure yanzu,yace a'a saboda shi student ne yagida ma yanzu hakuri take da yanayin rayuwa.to nabashi shawara akan ya haqura da yammatan da yake chatting da su azauna lafiya agidansa tunda ya nuna mun chart din yammatan ne ma ke nuna suna sonsa ma bashi ya yace yana sonsuba amma ya ki wai ba akin masoyi koda ba aurensu zaiyi ai ba'san inda rana zata fadiba toshine nakeson malam kabani shawara saboda kullum naje gidan saina sameta tana kuka.
(2) shin ya halasta mutum ya dinga soyayya da yammata a social media koda baya ra'ayin aurensu


 *AMSA*👇

Wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in. 

Shawara a nan bata wuce abinda kika yi ba, na kiran shi da tambayar shi ko yana da sha'awar kara aure ne, kuma ya baki amsa cewa baya da niyyar haka, hakan ya nuna cewa fajiri ne, yana haka don iskanci ne kawai. Wannan shine abu na farko. Yanzu shawara ita ce, ki bishi da nasiha da wa'azi ko ya yi aiki, ta hanyar tunatar da shi munin abinda yake yi a shar'ance, Allah baya son haka. Bayan haka, shi ma fa, zai haifa, kuma hakan na iya faruwa ga 'yar shi ko ba haka ba, zai iya faruwa ga 'yar uwar shi ko mahaifiyar shi, kuma tabbas ba zai so haka ba.

Idan bai saurare ki ba, toh dole ki hanzarta hada shi da iyayen ku domin su ladabtar da shi kan wannan bakar dabi'a da ya saka kan shi a ciki, na zance da 'yan matan mutane. Wannan mutumin banza ne tunda har yake dukan kirji cewa, 'yan matan ne suke son shi, ba shi ke son su ba, karya yake, domin ba shi bane Annabi Yusuf, kan kyau ba, ko Bill Gate, kan kudi ba, ko Rijiyar lemu a kan ilmi ba misali, ko PMB kan mulki ba, sannan ba dan autan samari bane, kawai fajiri ne, azzalumi. Bayan nan zancen shi cewa, ba'a san inda rana zata fadi ba, na nuna baya da shirin ya daina, idan ba haka ba kowa ya san cewa, rana zata fadi a yamma ne kamar a wajen mu nan, ma'ana wannan bakar mu'amala zina ce karshen ta, iyazhan billahi, duk mai hankali ya san haka, chatting shine asalin da za'a gina zina. Ya dauka chat ko zance da 'yan mata abu ne mai sauki, toh yana da girma a wajen Allah 

(إِذۡ تَلَقَّوۡنَهُۥ بِأَلۡسِنَتِكُمۡ وَتَقُولُونَ بِأَفۡوَاهِكُم مَّا لَیۡسَ لَكُم بِهِۦ عِلۡمࣱ وَتَحۡسَبُونَهُۥ هَیِّنࣰا وَهُوَ عِندَ ٱللَّهِ عَظِیمࣱ)
[Surah An-Nur 15]

Amma amsar ki ta biyu, shine bai halasta mutum ya dinga zance da 'yan mata ba a social media, Allah zai kama mutum da wannan laifin, Allah yace 

(أَمۡ یَحۡسَبُونَ أَنَّا لَا نَسۡمَعُ سِرَّهُمۡ وَنَجۡوَىٰهُمۚ بَلَىٰ وَرُسُلُنَا لَدَیۡهِمۡ یَكۡتُبُونَ)
[Surah Az-Zukhruf 80]

(مَّا یَلۡفِظُ مِن قَوۡلٍ إِلَّا لَدَیۡهِ رَقِیبٌ عَتِیدࣱ)
[Surah Qaf 18]

Allah na ji, sannan Mala'iku sun rubuta duk abinda suka zanta mai kyau da akasin shi, sannan Allah zai masu ukuba a kai kamar yadda Annabi sallallahu alaihi wa sallam yace, Allah na yafe zancen zuci ne banda aiki ko abinda harshe ya furta

1730 - «إن الله تعالى تجاوز لأمتي عما حدثت به أنفسها ما لم تتكلم به أو تعمل به» .
(صحيح) ... [ق 4] عن أبي هريرة [طب] عن عمران بن حصين. الإرواء: 2062.

Don haka chatting da 'yan mata ajanabiyya haram ne. Me zai hana shi ya dinga chatring da uwar shi ko kanwar shi, inna, goggo ko matar shi? Duk nan babu laifi. Mallamai sun ce hukuncin chatting daya da na khalwa, Annabi yace kar daya daga cikin ku ya kadaita da wata mace sai da muharramin ta, a wata riwayar yace hakan ba zai faru ba face shaidan ne na ukun su, kowa ya san haka

1909 - (10) [صحيح] وعن ابن عباس رضي الله عنهما؛ أن رسول الله - صلى الله عليه وسلم - قال:
"لا يخلون أحدكم بامرأة إلا مع ذي محرم".
رواه البخاري ومسلم.

Da yawan musulmi samari da dattijan su na daukar wannan abun na chatting, zuwa tadi, da friendship da 'yan mata, abu ne mai sauki, wallahi yana da girma a wajen Allah, domin shine kusantar zina da Allah ya hane mu

(وَلَا تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةࣰ وَسَاۤءَ سَبِیلࣰا)
[Surah Al-Isra' 32]

Bayan duk wannan akwai nauyin cuta ma matar shi da yake yi na bakan ta mata rai da saka ta kuka da huskantar bakin ciki da takaici, Allah zai saka mata, sai dai idan ta yafe masa. Annabi yace 

5062 - "لتؤدن الحقوق إلى أهلها يوم القيامة حتى يقاد للشاة الجلحاء من الشاة القرناء تنطحها [ ... ] حم م خد ت" عن أبي هريرة.
(صحيح) مختصر مسلم 1837، الصحيحة 1588.

Kar ya dauka yaci bulus, ba abinda zai faru karya yake.

Wallahu ta'ala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*


‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)