WANKAN JANABA


*SIFFAR WANKAN JANABA*

Tambaya :

Don Allah malam ina so a siffanta min yadda
ake yi wankan janaba, saboda ban jima da zama
mutum ba !

Amsa :

To dan'uwa janaba wani hukunci ne da yake
faruwa saboda daya daga cikin abubuwa guda
biyu : ko dai mutum ya yi mafarki kuma ya ga
maniyyi, ko kuma mutum ya sadu da matarsa,
duka wadannan suna wajabta wanka
Game da siffarsa kuwa, to wankan janaba yana
da siffofi guda biyu, duk wacce ka dauka ta yi :
.
.
1. Siffar da ta fi kamala ita ce wacce ta zo a
hadisin A'isha cewa manzon allah s.a.w. idan ya
zo wankan janaba yana farawa ne da wanke
hannunsa, sannan sai ya wanke farjinsa da
hannun hagu, sai kuma ya yi alwala amma ban
da wanke kafa, sannan sai ya debi ruwa sau uku
ya zuba a gashinsa, bayan haka sai ya zuba a
ragowar jikinsa, sannan sai ya wanke kafarsa.
Bukari da muslim.
.
.
2. Akwai kuma siffa ta biyu wacce ta zo a
hadisin Ummu-salama lokacin da Annabi s.a.w
yake siffanta mata wankan janaba, inda yake ce
mata : "Ya ishe ki ki zuba ruwa sau uku a kanki,
sannan ki zuba a duka jikinki, mutukar kin yi
haka to kin tsarkaka" Muslim ne ya rawaito a
hadisi mai lamba ta : 330.
Allah ne mafi sani.

Rubutuwa Dr. Jamilu Zarewa

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)