WAYE YA CANCANCI YIN LIMANCI?


Waya cencenci yin limanci?

https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA

 *TAMBAYA* ❓

Aslm Mlm barka da warhaka fatan kuna lafiya, inada tambaya ne ?
Waya cencenci yin limanci?

 *AMSA* 👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Wanda Yafi Cancanta Da Yin Limanci

Na farko : Wanda ya fi karatun Alqur’ani, wato wanda ya fi yawan haddace shi, kuma yafi sauran fahimtar hukunce-hukuncensa.

Na biyu : Wanda ya fi sanin Sunnah, wato wanda yasan ma’anoninta da hukunce-hukuncenta.

Na uku : Wanda ya dade da yin hijira, daga garin kafirci zuwa garin musulunci. Idan ba hijira a lokacin sai a gabatar a kan wanda ya riga tuba da qaurace wa sabo.

Na hudu : Idan su yi daidai a duk abin da ya gabata, to sai a sa wanda ya fi yawan shekaru.

Dalili akan abin da ya gabata hadisin Abu Mas’ud Al-ansari – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya fi mutane karatun Alqur’ani shi zai limance su, idan sun yi daidai a karatu, to wanda ya fi su sanin sunnah, in sun yi daidai a sanin sunnah, to wanda ya fi dade wa da hijira, idan sun yi daidai a hijira to wanda ya dade da musulunta” [Muslim ne ya rawaito shi].

Ana kula da wannan jerin yayin maza limamin masallaci, ko in a cikin jama’a ne waÉ—anda babu lmami ratibi a cikinsu, in akwai limami a ratibi a cikinsu, ko kuma wanda ake gidansa yana nan, ko kuma wanda yake jagora to shi za a gabatar da wanda ba shi ba [Kamar a ce sarki ne ko shugaban wurin da makamancinsa] ,

saboda faÉ—in Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Kada wani mutum ya yi wa wani mutum limanci a wurin ikonsa, kada ya zauna a wurin zamansa a gidansa [Wurin zamansa, shi ne wurin da aka tanadarwa baqo don ya zauna], sai dai da izininsa” [Muslim ne ya rawaito shi].

WALLAHU A'ALAM

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)