*BANBANCIN ZINAR IDO, DATA JIKI DA JIKI :*
.
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
.
_*TAMABAYA*_❓
.
_Assalamu alaikum Dafatan An Wuni lfy Malam dama tambaya Nike Akan Hukuncin Zinar ido ta hayar kallon abinda yake na haramu ,Kuma da Banbancin dake tsakanin Zinar jiki data ido._
:
_*AMSA*_👇
:
_Zinar ido (wato kallon abinda Allah ya haramta) da kuma zinar jiki da jiki, dukkaninsu laifuka ne masu girma. Domin kuwa Allah ya haramtasu acikin Alqur'ani da kuma hadisai ta harshen Annabinsa ﷺ._
_Zinar ido tana daga manyan hanyoyin da Shaitan yake bi domin jan mutane zuwa ga aikata zinar jiki da jiki._ _Shi yasa ma Allah yace wa Annabinsa ﷺ "Ka gaya wa muminai maza su runtse idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu, wannan shi yafi tsarkakewa gareku. Hakika Allah masani ne game da abinda suke aikatawa"._
_Imam Ibnu Katheer yace : "Wannan umurni ne daga Allah (SWT) zuwa ga bayinsa Muminai cewa su runtse idanuwansu daga kallon duk abinda ya haramta musu. Kada su kalli komai sai abinda ya halatta musu kallonsa"._
_Manzon Allah ﷺ ya fa'da acikin wani hadisi cewa "Kallo, wani kibiya ne mai dafi (poison) daga kibiyoyin iblees. Duk wanda ya barshi (wato ya bar kallon) domin tsorona, zan chanza masa da wani imani, zai ji dandanonsa acikin zuciyarsa"._
_(Tabaraniy ne ya ruwaitoshi)._
_2. Ita kuwa zinar jiki da jiki, ai Manzon Allah ﷺ yace "Bayan yin shirka da Allah, babu wani zunubi mafi girma kamar maniyyin da wani mutum ya sanya acikin mahaifar da bata halatta gareshi ba"._
_Kuma yace "Mazinaci ba zaiyi zina alhali yana mumini ba". (Wato sai bayan an cire masa imani)._
_Zinar ido babu haddi akanta. Amma zinar jiki da jiki, in dai shaidu suka tabbata akan masu laifin, ko aka samu Iqirari tabbatacce daga masu laifin, ana yi musu haddin bulala dari (100) idan basu ta'ba aure ba. Idan kuma sun ta'ba yin aure hukuncin rajamu ake musu (wato jefesu da duwatsu har sai sun mutu)._
_Kuma Manzon Allah ﷺ ya bada labarin dake nuna cewar koda acikin wuta, mazinata wajen azabtar dasu ya bambanta, yafi muni fiye da na sauran 'yan wuta. (Allah shi kiyayemu da aikata zina, kuma ya kiyayemu daga shiga wuta)._
:
```Allah ta'ala yasa mudace```
:
_*©✍🏽 Sadeeq Ñagogo{βluñgu}*_
:
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕