NA KASANCE MAI ƘARFIN SHA'AWA TUN TASOWA TA

*NA KASANCE MACE MAI ƘARFIN SHA'AWA TUN TASOWATA* 

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
.
 *TAMBAYA* ❓
:
Assalamu alaikum inama malan fatan alkhairi dan allah shawara nake nema nakasance mace mai karfin sha'awa tun tasowata gashi iyayena waisai munyi karatu me xurfi hartakaiga inasa hannu a farjina idan nasa nakanji kwanciyar hankali kuma idan nayi istigfari akan natuba sai nakoma saboda wahalar ciwon da nakeji natuba yafi sau nawa dan allah aban shawara nagode
:
 *AMSA* 👇
:
Wa'alaikumussalam warahatullah
To 'Yar uwa wannan matsalar tana damun matasa maza da mata wato matsalar rashin Aure, kuma wannan sa hannu a farji, sa6awa ALLAH ta'ala ne, gaskiya kuma shawaran da nake baki anan itace.
:
Na farko kidena zama a Daki ke kadai Sannan ki yawaita Azumin nafila domin Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) yace yana rage qarfin sha'awa
.
Sannan ki yawaita karatun Alqur'ani shima wannan babban magani ne Ki yawaita Istigifari, kuma shi qofar tubanki tana nan a bude kamar yadda wannan hadisin ya nuna
 كل بني ادم خطاء وخير الخطاءين التوابون
"Dukkan 'yan adam masu sa6one, mafi alherin masu sa6o, sune masu tuba"
:
Dan haka ki tuba kiyi nadama akan cewa bazaki qara komawa zuwa ga wannan sa6on ba Insha ALLAHU, ze yafe miki 
.
Anan muke kira ga iyaye wallahil azeem kuji tsoran ALLAH idan anzo neman Auren 'yayan ku, Ku bayar idan ba haka ba wallahi zaku haifar da fitina a bayan qasa domin a sanadin kaqi yiwa 'yarka Aure taje ta fada ZINA !! to lallai kai ne sanadi kuma kanada naka kason Na zunibi.
.
Duk Wanda akazo Neman Aure Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) yace: Ku kalli addinin sa kawai Ku bashi idan kunqi fitina zata haifu a ban qasa.
.
Wallahi sa6awa maganar Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) dedai yake da sa6awa ALLAH.
.
ALLAH ta'ala ya tsaremu
:
✍🏽 ​​Sadeeq Ñagogo{βluñgu}​​​​
:
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕


Post a Comment (0)