AN SAKA MUSU RANAR AURE, YARINYAR DA YAKE SO TA FITA DAGA RANSA, WAI WATA YAKE SO
https://chat.whatsapp.com/LRPQDrs7qSoKXuSspoPkFm
*TAMBAYA*❓
Assalamualaikum
Malam barka da Asuba
Dan Allah malam shawara muke nema abisa abinda ya daure mana kai
Abokina ne yana neman Aure tsawon shekara 3 har ansaka musu ranar Aure lokacin ya kusa.
To malam yanzu sai yazo wajena yake neman shawara ta yana cewa gaskiya yanzu yaji yarinyar ta fita daga ransa baya sonta
Sai yakece min yanzu shi yar uwarta yake so kakar su daya da wadda aka samusu ranar kuma shima dan uwan sune.
Malam na bashi shawara kan idan yayi haka bekyauta ba kuma zai iya haifar da gaba a tsakanin su.
Kuma ita waccan yarinyar ya bata mata lokaci tsawon shekara 3 bata kula kowa sai shi.
Duk iyaka yabanin dazan yi masa nayi amma shi yace bayin kansa bane Allah ne kawai ya jarab ceshi da son wannan yarinyas gsky yana matukar sonta
Kasan cewar tana da Ilimin Addini fiye da waccan
Malam ina neman wasu wujjojin da zan kara fada masa ko zai yarda da magana ta.
Malam Idan ya koma wajan waccan din bashi da lefi ko a wajan Allah?
Nagode malam Allah yayi jagora Amin.
*AMSA*👇
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
Allah ya sanyawa dan Adam son Mace. Haka an sanyawa Mace son Namiji.
Kenan idan ya ce soyayyar Waccan ta Fita daga Ransa. To ina mai Sanar da shi cewar idan ya ga wata ma haka son ta zai shiga Zuciyar sa. Haka so yake. Amma a haka kowa yake gani kuma ya ji Abin a Zuciyarsa Sannan kuma a haka zai Hakura. Hakan su ma matan.
Kuma idan har haka Zuciyarsa take, da Alama zai zama Namiji Mai Auri-saki.
Sabida duk Matar da ya Aura. Zai ji ta Fita a ransa. Sai ya sake ta ya Auro wata. A haka zai gama Rayuwar sa ya zama Abin Zargi kenan a wajen AL'UMMA. Har sai an wayi Gari kuma ana hana shi Aure. Sabida An san idan an bashi Aure sakawa zaiyi.
Ka ce ya Tambaya ya ji. Kowanne Namiji haka ya ke ji a Zuciyarsa. Amma. Haka yake Hakura. Wani lokacin ma Mutum zai ga Kanwar matarsa da suke Uwa daya Uba daya. Kuma ya ji yana Tsananin son ta. Amma babu yadda zaiyi. A haka zaiyi Hakuri. Shi Daman SO haka yake.
Sabida haka ka ce masa in jini yayi Hakuri. Ba Namijin da ba ya jin Wannan a Zuciyarsa.
Kuma idan yayi haka ma ae ya Zalunce ta, ya Cuceta. Kuma ya cuci Rayuwar ta. Sannan babu wadda zai aura wannan Auren Nasa yayi Albarka.
Maganar zai auri Yar Uwarta. Shine yake ganin hakan. Amma ya gwada ya gani. Ba zasu Amince ba. Mata fa ba sa Amincewa da haka.
Mace ce fa Zaka yi soyayya da wadda ta sani. K je wajen ta taki amince maka. Bare kuma ka je wajen wadda suke danginsu daya.
Ban ki hakan ba Idan har an sami matsalar ne daga gare ta. Ma'ana idan har itace ta ce ba ta son ka. Haka zai Iya yiwuwa. Amma Kaine kake son ka Jefa kanka Cikin Matsala. Kuma abinda kake Tsammanin ba zai yiwu ba.
Sabida haka zaka yi Biyu-babu.
Allah shine Masani.
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕