AYATUSH SHIFA'I (AYOYIN SAMUN WARAKA)



AYATUSH SHIFA'I (AYOYIN SAMUN WARAKA)

https://chat.whatsapp.com/BsuVPYdzZY7C1Sv0lgoNES

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum dan allah mlm ayoyin waraka zaagayamin ayatush shifa
Ngd allah kara ilmi mai anfani

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Wadannan sune ayoyin da ake kira AYATUSH SHIFA'I (Ayoyin Waraka) Mutane su rika amfani dasu acikin sha'anin Magungunan Musulunci.


1. Ayah ta 14 acikin Suratut Taubah.
2. Ayah ta 57 acikin Suratu Yoonus (as).
3. Ayah ta 69 acikin Suratun Nahli.
4. Ayah ta 82 acikin suratul Isra'i.
5. Ayah ta 80 acikin suratush Shu'ara.
6. Ayah ta 44 acikin Suratu Fussilat.

Duk wanda yake fama da wata jinya acikin jikinsa zai iya karantasu ya tofa acikin ruwa sannan ya rika sha, da kuma shafawa ajikinsa. In sha Allahu Za'a samu waraka daga Allah.
An nakalto daga wani babban Malami daga cikin Malaman Musulunci wato Shaikh Abul Qasim Al-Qushairiy (rah) cewa dansa yayi rashin lafiya mai tsanani. Yace:
"Na fidda tsammani daga warkewarsa, Kuma al'amarin yayi tsanani gareni. Sai naga Manzon Allah (saww) acikin Barci. Da na gaya masa abinda ke damun yarona sai yace mun "MAI YASA BAKAYI AMFANI DA AYATUSH SHIFA'I BA?".
Bayan na farka daga barcin, Nayi tunani sosai sai na gano cewar ashe ayoyin suna nan agurare shida ne daga cikin Littafin Allah". 

"Da na rubuta masa ajikin Farar takarda, na wanke da ruwa na bashi yasha, sai ya tashi kamar wanda aka kunceshi daga Igiya" (Wato ya warke nan da nan).

Don haka ina jan hankalin 'Yan uwa Musulmai cewa kuyi amfani da wadannan ayoyin ku rubuta da abu mai tsaeki akan abu mai tsarki, Sannan ku sha. Ko kuma ku rika tofawa acikin ZAM-ZAM kuna sha.

Wallahu A'alamu

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: 👇_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)