AL'AMARIN MACE SAI ALLAH



Al'amarin mace sai Allah da ya halicce ta sai kuma wanda Allah ya kare.

Za ka ga mutum mai ƙoƙarin ibada da kuma kamewa daga manyan zunubai yayi nasara a kan shaiɗan amma sai shaiɗan yayi galaba a kan sa ta hanyan mace. Kamar yadda wani magabaci yake cewa tarkon mace ne kawai shaiɗan idan ya sa wa mutum ya tsallake, shaiɗan ɗin ya ke sallama wa a kan yafi ƙarfin sa.

Don haka Annabin Rahama s.a.w. yake cewa...

قال رسول الله ﷺ: ما رأيت من ناقصات عقل ودين أغلب للب الرجل الحازم من إحداكن

"Ya ce ban taɓa ganin halitta mai tawaya a hankali da addini kuma mai galaba a kan hankalin haziƙin namiji irin ku ba"

Shi ya sa Allah da ya zo hana zina ba cewa yayi kar kuyi zina ba, a'a Allah cewa yayi kar ku kusanci zina, saboda shi Allah ya sani idan a ka kusan ta to imani da ilimi ba sa aiki, shi ya sa Annabin Allah Yusuf shima sai da Allah ya kawo masa ɗauki.

Ashe maganin bari kar a fara, tunda Allah ya haramta kaɗaituwa da macen da ba muharraman ka ba to kayi ƙoƙari ka kame ko ta hanyan waya ne don shima wani tarkon ne.

Shi yasa tsarin musulunci kullum shine a nisantar da numfashin maza da ga mata, don haka nema yace...

مَا تركْتُ بعْدِي فِتْنَةً هِي أَضَرُّ عَلَى الرِّجالِ مِنَ النِّسَاءِ

" Ban bari a baya na ba wata fitina wadda take da tsananin cutarwa ga maza ba kaman mata"

Su kuma yahudawa tun da matan su sun ta re sun koma kan titi sai ya zama duk tsarin su a kan mu shine matayen mu su dawo kan titi kaman na su, kuma da alama sunyi nasara.

Allah ka yafe mana ka azurta mu da kamewa.

*Ahmad Muhammad Makama.*

*📚Irshadul Ummah whatsApp.*
*+2348166650256.*

https://t.me/irshadulummah1
Post a Comment (0)