HAƘURI AGIDAN MIJI ZAI GADAR MIKI KARSHE MAI KYAU DA KUMA NASARA DUNIYA DA LAHIRA.



HAƘURI AGIDAN MIJI ZAI GADAR MIKI KARSHE MAI KYAU DA KUMA NASARA DUNIYA DA LAHIRA. 

Shaykh Uthaimeen Allah ya masa rahama yana cewa; "Idan har mata ta yi hakuri ta nemi lada awurin Ubangijinta sannan tayi dakon mafita daga wurin Allah, takuma sauke hakkin mijinta da Allah ya dora mata koda kuwa shi mijin ta tauye mata nata hakkin, to lalle nasara da kyakykyawan karshe na gareta. Wanda kuma wannan ita ce qa'ida ga duk wanda yake da hakki akanka, idan har kai ka sauke naka hakkin shikuma yaki saukewa to sai Allah ya doraka akansa. 

   Dalili kuwa hadisin Manzon Allah, wanda sahabi Abi huraira ya ruwaito ya ce, "Wani mutumi ya zo wurin Manzon Allah ya ce: Ya manzon Allah na kasance ina da yan uwa wadanda ina sadar musu da zumunci amma su suna yankemin, ina kyautata musu, amma su suna munantamin, ina hakuri dasu amm su sunamin jafa'i. Sai Manzon Allah ya ce, masa "Idan har ka kasance kamar yadda ka fada to kananan kamar kana ciyar dasu tokace Mai zafi, kuma bazaka gushe ba Allah yana baka kariya da taimako ba har abada matukar kananan ahaka baka sauya ba"

مسلم ٢٥٥٨ 
#Zaurenfisabilillah 

Telegram:
 https://t.me/Fisabilillaaah

Facebook:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/
Post a Comment (0)