KISSAR WANI MATASHIN SAURAYI




KISSAR WANI MATASHIN SAURAYI
.
=
..*DAGA ZAUREN
*📗ADDINI DA RAYUWAR DAN ADAM GROUP📗*
08186761010 ** 09038090522
.
_Wata rana wani bawan Allah matashin saurayi yana kwance da daddare yana bacci a dakinsa Kwatsam sai wata yarinya ta kwankwasa masa kofa dare ya tsala ana ruwa domin ya bata mafaka, shikenan kawai sai wannan bawan Allah ya bata mafaka a cikin dakinsa shikenan wannan yarinyar ta kwanta bacci. To Sabida yadda shi wannan matashin saurayin yaga Allah yayiwa wannan yarinyar 'kira mai kyau, Sai kawai ya kunna wuta a cikin dakin ya dinga kara hannunsa a jikin wutar sabida kawai wannan wutar ta dinga tuna masa azabar lahira sabida kada ya zamanto ya sabawa Allah ta hanyar ketawa yarinyar mutuncinta, haka ya dinga kara hannunsa a wannan wutar tana konashi har wayewar gari, bayan wayewar gari yarinyar ta tafi abinta._
.
_Wani ikon Allah subhanahu wata'ala Sai da Allah madaukakin sarki daga baya ya 'kaddara ita wannan yarinyar ta zama matar shi wancan matsashin._
.
_Darasi:_
_Duk yadda zuciyarka ta raya maka sha'awar wani abu to kar ka kuskura ka nemi abin ta hanyar haram, kayi hakuri ka nemi taimakon Allah da sannu Allah zai kaddara maka samun Abin ta hanyar halal. da wancan matashin yayi hakuri Sai Allah ya aura masa matar sai ya sameta ta halal._
.
_(Ihifazullaha yahfazuka ka kiyaye Allah Zai kiyayeka) Da matashin ya kiyaye Allah alokacin sai Allah ya kiyayeshi be nemi yarinyar ta hanyar haram ba._
.
_(Waman yattaqillaha yajAllahu makhraja) Kuma wanda yaji tsoron Allah Da sannu zai kawo masa mafita. Idan kaji tsoron Azabar Allah ka nisanci saba masa, dasannu zai kawo maka mafita._
.
..
_Wallahu A'alam_

_ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ._ 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)