KU RIQA SHAN NONON SANIYA AKWAI WARAKA ACIKINSA
Manzon Allah SAW shine;Babban likitan duniya baki daya wanda har yanzu ilimin likitancinya yana nan har ana amfana da shi har zuwa gobe alqiyma.
Manzon Allah SAW yayi mana umarni da Shan Nonon Saniya domin akwai samun waraka acikinsa da yardar Allah.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;
(Lallai Allah mai girma da buwaya,bai taba saukar da wata cutaba,face ya saukar da maganinta,sai da mutuwa,dan haka na kwadaitar da ku akan shan nonan Saniya,domin ita tana ci daga dukkan itaciyoyi)
@صححه الألباني في السلسلة الصحيحة -رقم:(518)
A wata Riwayar Manzon Allah SAW yana cewa;
(Ina kwadaitar da ku akan shan nonan saniya domin nonanta warakane,......kuma nayi maku kashedi daga Namanta,domin namanta akawai cuta)
@صححه الألباني في صحيح الجامع - رقم:(4061)
Malamai suna cewa dukkan abinda Manzon Allah SAW ya fada na magani tabbas hake yake babu kokwanto acikinsa.
Amfanuwa daga wannan magani yana da alaqa da Imaninka da qakininka ya yardarka da gaskatawarka ga Manzon Allah SAW.
Allah ne mafi sani.