Annabi (ﷺ) Ya fi Kowa Iya Koyarwa:



Ramadaniyyat 1442H [10]

Dr. Muhd Sani Umar (hafizahullah)

Annabi (ﷺ) Ya fi Kowa Iya Koyarwa: Shaidar Mu'awiya Dan Al-Hakam As-Sulami
_____________________________
1. Wannan ita ce shaidar da Mu’awiya dan Al-Hakam As-Sulami ya bayar, lokacin da ya shiga masallaci yayin da ake yin salla, sai ya ji wani ya yi atishawa, sai ya ce masa: 'Yarhamukallah'. Sai sahabbai suka harare shi, don su nuna masa ba a irin haka ana salla. To a lokacin sai yake magana yake cewa; ya aka yi na ga kuna ta hararata? Sai suka fara daga hannayensu suna bugun ciyoyinsu, alamar suna nuna ya yi shiru, sai ya shiru. To da aka yi sallama sai yake cewa: "Mahaifina da mahaifiyata fansa ne gare shi (wato Annabi (ﷺ))". Ya ci gaba da cewa: "Tunda nake ban taba ganin wani malami gabaninsa ko bayansa wanda ya kai shi iya koyarwa ba". Ya ce; bai daka min tsawa ba, bai hantare ni ba, ballantana ya dake ni, sai dai kawai cewa ya yi da ni: "Ita wannan salla babu wani abu na zancen mutane da ya dace a cikinta, ita salla tasbihi ne da kabbara da karatun Alkur’ani kadai". [Muslim#537].
2. Wannan shaidar da Mu’awiya dan Al-Hakam ya bayar ita ce shaidar da duk wani mai adalci zai bayar game da Annabi (ﷺ), watau cewa duk duniya ba a tava yin wanda ya iya koyarwa da karantarwa kamar Annabi (ﷺ) ba.
3. Wannan shi zai tabbatar da cewa, wadanda suka zauna da shi, su suka fi kowa gaskiya da iya mu’amala, saboda sun samu tarbiyya daga wanda ya fi kowa iya bayar da tarbiyya.
4. Don haka idan ana so a fito da matsayin Annabi (ﷺ) ga wadanda ba su san wane ne shi ba, sai a nuna musu darajar sahabbansa, da yadda suke a farko kafin su shiga Musulunci, da kuma yadda suka koma bayan sun karvi Musulunci. Yadda suka koma masu gaskiya da amana da kaunar juna da rahama da tausayi. Wannan shi ne zai kara tabbatar da girman Manzon Allah (ﷺ) da girman abin da ya zo da shi. 
5. Idan kuma wani yana so ya soki Annabi (ﷺ), to babu abin da zai fada fiye da ya soki sahabbansa, ya nuna cewa, su wasu mutane ne maha’inta, marasa gaskiya. Domin yin wannan tuhuma a gare su, suka ne a fakaice ga shi wanda ya ba su tarbiya, don sun zauna tare da shi tsawon shekaru ashirin da uku (23), amma ba su sami kyakkyawar tarbiyya ba. Babu shakka wannan suka ne na gaske ga shi kansa ya rene su, watau Annabi (ﷺ).


https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)