BAMBANCI {26}



BAMBANCI {26}

SANA-MAKKEY (TAFASA)

*SANA-MAKKEY ko TAFASA da Hausa ko SENNA da turancin Ingilishi,* tana daya daga cikin itatuwan da Nassi yayi bayaninsu cewa suna maganin dukkanin cututtuka banda mutuwa, itama Tafasa haka Hadisai suka yi bayaninta, Sana-Makkey ta fi shahara a kasashen larabawa da hausawa wajan amfani da ita ga magungunan cututtuka iri-iri, ciki har da sihiri.

A kasar hausa an saba dafa ta a ci ko a kwadanta ta da quli, amma wasu da dama ba sa yarda su dafata ita kadai sai dai su hada ta da wani ganyen kamar zogale/zogala da sauransu domin ba a so ne aci ta tayi yawa a ciki sai ta iya kawowa mutum matsala a jikinsa.

A bangaren lalata sihiri kuma Tafasa kam tana matuƙar taimakawa Allah ya warkar da wanda aka yiwa sihiri ko wanne irin nau'in sihiri ne kuwa cikin iko da yardar Allah. Mutane da dama na amfani da ita ta fannoni da hanyoyi mabanbanta, amma hanyar amfani da Tafasa wajan warware sihiri ko lalata shi da masana suka ce ta fi karfin aiki itace kamar haka:

1- Za a samu ganyen Tafasa iya adadin wanda zai cika maka tafin hannu ko adadin gram 5, sai ka tsaftace ta bayan ka tsaftace ta sai ka sanya ruwa kimanin kofi 1 sai ka dafa su tare (amma zai kyautu ace ka sanya ganyen na'a na'a, ko Qirfa, ko kanumfari kadan a ciki, saboda su dan sauya mata wari da kuma dandanon don tayi dadin sha a baki da harshe.)

Bayan ta tafasa sai ka sauke ka tace sai ka sanya zuma a kalla babban cokali 1, sai ka sha kafin kayi karin kumallo a shekarar sau 2 za kasha, a sati na 2 kuma sai ka sanya ruwa kofi 2, sai ka sha sati na uku ma kofi 1, sati na 4 kuma kofi 2, kimanin wata daya kenan, sai akara na wani wata 1 ya zama wata 2.

Insha ALLAHu, duk wanda akayiwa sihiri ko yaci sihiri ko guba da izinin ALLAH kafin wata biyun zai samu lafiya cikin iko da yardar Allah , sai dai kuma wani ikon Allah.

*GARGADI...*

A duk ranar da ka sha maganin yakasance kana shan ruwa akai akai saboda malamai sun bincika cewa TAFASA tana saukar da kitsen da ke jikin mutum sauka ta ban mamaki, shi yasa akace a rika shanta sati sau 1, saboda kar a samu matsala, wasu suna amfani da ita wajan rage kitsen da ke a jikin mutum idan aka daka garin aka debi cokali 1 aka dafa shi da ruwa kofi daya ana sha da zuma kullum da safe a sati sau 2 kuma mutum yarika motsa jiki, Insha ALLAHu zai rage kitsen da ke jikinsa.

A rubutu nagaba za muji ci gaban insha ALLAHu...

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)