AMARYA

AMARYA



Wata Amarya ce bayan an daura mata aure,dare yayi lokacin za'a kaita dakin mijinta sai kuka takeyi ita bata zuwa ta fasa Auran da kyar aka samu aka sakata a mota tanata kuka. Aiko ana zuwa unguwar sai direban ya manta gidan,kuma duk wayanda suke motar basu san gidan ba,chan sai wata tsohuwa tace "kawai a koma da ita gida,gobe angon yazo yatafi da ita" Amarya tanajin haka, kuma taga direba ya juya zai koma da ita gidansu kawai sai tabar kukan datake tace "GAFA GIDAN CHAN MAI FARIN FANTI" Ahahaha wai in kune a Motar Amaryar nan me zaku ce Mata???

 
Post a Comment (0)