GULMA HATSARI NE!!!

GULMA HATSARI NE!!! 






Sahabi Anas bin Malik Allah ya ƙara masa yarda yana cewa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wa sallama yana cewa: "Alokacin da akayi mi'iraji dani, na wuce wasu mutane masu faratu dogaye na ƙarfe suna ta yagunan/yakushan fuskarsu da ƙirjinsu, sai na tambayi mala'ika jibril shin suwaye waɗannan?? Sai yacemin waɗannan sune masu cin naman mutane da cin mutuncin su".
  صحيح أبي داود ٤٨٧٨

Shaikhul Islam Ibnu Taimiya Allah ya masa rahama yana cewa "Duk wanda ya zalunci wani mutum ya masa ƙazafi ko yayi gulmansa ko ya zageshi sannan ya tuba to Allah zai yafe masa, idan kuma yasan wanda ya zalunta to ya bashi daman karbar haƙƙinsa, amma idan ya masa qazafin ko yayi gulmansa amma labari bai iske wanda akayiwan ba to akwai maganganu guda biyu na malamai, Dukansu ruwayoyi ne daga Imam Ahmad, wanda yafi inganci acikinsu shine: bazai sanar dashi ba, wasu kuma sukace yaje ya faɗi alkhairinsa awurin da ya ɓatash, kamar yadda Imam Alhassanul basari ya faɗa "kaffarar gulma shine neman gafarar wanda akayiwa".

مجموع الفتاوى ٣/٢٩١

@Niamey#Niger_Republic

  #Zaurenfisabilillah 

TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah

FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/
Post a Comment (0)