💰 Roqo.... 💰
.
.
🌴 عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: *((مَنْ سَأَلَ النَّاسَ أَمْوَالَهُمْ تَكَثُّرًا فَإِنَّمَا يَسْأَلُ جَمْرَ جَهَنَّمَ فَلْيَسْتَقِلَّ مِنْهُ أَوْ لِيُكْثِرْ)).*
📒 [ابن ماجه /١٩١١]
.
🌴 Dãgã Abí Huraira (Ra) yace: manzon Allah SAW yace: *"duk wanda yake roqon mutane dukiyarsu domin ya tara (bawai don wata larura ba) to ya sani kamar yana roqon garwashin wuta ne na jahannama, ya rage nasa yayi kadan ko yayi da yawa"*
.
👉🏻 Hakika Kamewa daga roqo wani abu ne da Allah yake so.
👉🏻 Shakka-babu ana cikin wani hali na quncin rayuwa, amma kayi iya qoqarinka don kaga baka roqi kowa ba, matuqar bawai ya zama dole ba.
👉🏻 Ka zamlnto mai boye babunka har mutane su fara maka kallon mawadaci. Domin irin wadannan mutane masu kamewa sune suka fi cancanta a taimakawa idan aka gane hakan.
.
👉🏻 Shi yasa idan dan adam ya samu wadatar zuciya hakika ya samu wadata mai albarka, domin manzon Allah SAW yace:
*"ليس الغنى عن كثرة العرض ولكن الغنى غنى النفس"*
*"Ba shine wadata ba ace mutum yana da tarin kaya (dukiya), sai dai wadata ne ace mutum yana da wadatan zuciya."*
_🤲🏻 Allah ka azurtamu da wadatan zuciya Kuma ka rabamu da taulaci mai tozartarwa._
SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
