TAMBAYA ======== 👇
Assalamu alaikum malam inayi maka fatan alkairi, malam tabayata anan ita ce, za kana ganin hotuna a wayoyi ko a jikin takarda ance wannan hoton takalmin annabi ne ko kuma ace wannan rigar annabi ce s,a,w ko kuma hula ko rawani ko hoton sawun kafa, to malam wai shin wadanna dagaske su dinne kuwa, duba da a wancen lokacin babu camera, shine aduk lokacin da naga irin wannan hotunan a waya sai ina ta wasi wasi, a huta lfy Malam.
AMSA ===== 👇
Gaskiya ba Su bane. Kawai mutane ne Sabida sun San hankalinmu akan manzon Allah (s.a.w) yake, sai suke amfani da wannan damar suke yawo da hankullanmu gabaki daya. Ta yaya a zamanin da babu kyamara wani zaizo Maka da wani hoto yace Maka wai takalmin manzon Allah (s.a.w) ko rigar manzon Allah ce wannan? Wani ma sai kaga ya dakko hoton wani mutum da yayi mummunan hadari jikinsa ya rididdige, sai ya rubuta a kasan wannan hoton ko yayi recording yace wannan mutumin yaci mutuncin manxon Allah (s.a.w) ne ko ya zagi manzon Allah saw, Allah ya maidashi haka. Kuma babu inda hakan ya faru, domin babu wata jarida da ta buga wannan rehoton, bare kace ga inda abin ya faru. Kuma ma sai Kaji mutum yace idan mutum bai yaɗa Wannan labarin ba Allah zai saukar masa da wani bala'i, kamar wanda akayi masa wahayi akan wannan sakon da yake kokarin yaɗawa al'umma. Kaga irin waɗannan mutanen da suke kirkirar karya suna yaɗawa, wani Lokacin ma har barazanar suke yiwa mutane with, wai in baka turawa mutum goma ba bala'i zai sameka, Su kuma mutane da yake akwai jahilci da duhun kai a wurinsu da rashin wayewa, sai kaga mutum tana ta yaɗawa a group da Kuma duk wanda ya sani sai ya tura masa. Wai shi dan ya kubuta daga bala'i da zai sameshi idan bai tura ba. to wallahi wutar irin waɗannan mutanen daban take a ranar Alkiyama. Kuma Allah bazai kyale irin wannan iskancin ba. Domin renawa mutane hankali ne.
Allah shine masani.
✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
