SUJJADAR QABLI



SUJJADAR QABLI
-
Abdullahi Bin Buhainah (R.A), Sahabin Manzon Allah ne, yace:
"Wata rana muna sallah tare da manzon Allah (S.A.W) sallah mai raka'o'i hudu, sai muka yi raka'a biyu, sai muka ga ya miqe zuwa raka'a ta uku, ya manta bai zauna yayi tahiyar farko ba, sai ya cigaba da sallar kawai, muma muka bishi, bayan mun yi raka'o'i hudu, sai aka zauna aka yi Tahiyar 'karshe, muna zaune muna jira muji manzon Allah yayi sallama, sai muka ga bai yi ba, sai ya sake komawa 'kasa, ya kai goshin sa yayi sujuda guda biyu daga zaune (bayan yayi tahiyar 'karshe)".
.
"Sai muma muka bishi muka yi sujuda biyu, yana 'dagowa daga sujudar sai muka ji yayi sallama, sai muma muka yi sallama".
Wannan itace sujudar Qabli.
Ana yinta ne duk lokacin da aka mance wani abu a sallah, wanda yake rukuni ne na sallar.
Za ayi sujuda biyu bayan an kammala Tahiyar 'karshe, idan aka dago daga sujudar kuma ba za'a sake yin Tahiya ba, sai ayi sallama kawai, da ikon Allah idan kayi haka sallar ka ta gyaru.
.
Ba'a sake Tahiya, idan ka sake yin Tahiya toh ka mai-maita Tahiya biyu a zaune kenan, wanda kuma babu dalili akan haka daga al-Qur'ani ko Sunnar manzon Allah (S.A.W).
[ "Fiqihus Sunnah Lin Nisaa'" na Abu Malik Kamal, a shafi na 151.
Sahihul Bukhariy, Hadisi na 1,224].
-
Telegram
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Instagram
https://mobile.facebook.com/Hausa-Islamic-Pictures-Quotes-304897013359792/?ref=opera_speed_dial_freefb
Post a Comment (0)