SUNNONIN DA AKA MANTA DA SU, DAGA CIKIN SUNNONIN RANAR JUMA'A



SUNNONIN DA AKA MANTA DA SU, DAGA CIKIN SUNNONIN RANAR JUMA'A 

⭕Daga Cikin Sunonin Ranar Juma'a Da Aka Manta Aiki Da Su Akwai: YIN SALLAR NAFILA BAYAN JUMA'A RAKA HUDU A MASALLACI KO RAKA'A BIYU A GIDA KO RAKA'A HUDU A MASALLACI BIYU A GIDA⭕

🔆Daga Abi Hurairata رضـﮯ الله عنه Daga Manzon Allah ﷺ Yace: (Idan Ɗayanku Yayi Sallar Juma'a To Yayi Nafila Raka'a Hudu A Bayan Sallar Juma'a)
@صحيح مسلم ٨٨١

Daga Abdullahi Bn Umar R.A Daga Manzon Allah Saw Ya Kasance : {Baya Yin Sallar Nafila Bayan Sallar Juma'a Har Sai Ya Yi Insirafi, Sai Ya Yi Sallah Raka'a Biyu}
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 937 ‏) ، ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( 882 ‏) 

🔆ابن القيم رحمه الله :
Yana Cewa:
Malamin Mu Abbul Abbas Ibn Taimiya Allah Ya Yi Masa Rahama Yana Cewa: {Idan Mutum Zai Yi Nafilar Bayan Sallar Juma'a A Masallaci To Sai Yayi Raka'a Guda Hudu, Idan Kuma A Gida Zai To Sai Yayi Raka'a Biyu}.

🔆(ابن القيم)
Yana cewa 
"Yin hakan shine aiki da dukkan hadisan guda biyu.
 
Abu Dauda Ya Ruwaito Daga Abdullahi Bn Umar Ya Kasance: {Idan Zaiyi A Masallaci Yana Yin Raka'a Hudu Idan Kuma Zai Yi A Gida Sai Ya Yi Raka Biyu Kadai}. 
📓زاد المعاد(1/417) .

          Allah Ne Mafi Sani

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)