HUKUNCIN FAƊIN (JUMA'AT MUBARAK)



HUKUNCIN FAƊIN (JUMA'AT MUBARAK)

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum. Dr ko ya halatta Musulmi yayi wa dan'uwansa murna da zagayowar juma'a ta hanyar sako a wayar sailula kamar ace JUMA'A KAREEM ko JUMA'A MUBARAK? Allah yaqara sani.

*AMSA*👇

Wa'alaikum assalam, Akwai malaman da su ka hana hakan, suna ganin ba shi da asali a addini, Amma abin da yake zahiri hakan ya fi kama da al'ada, wannan yasa haramta shi yake bukatar Nassi, tun da babin al'adu da mu'amaloli a bude yake, sai abin da sharia ta haramta. Duk Wanda yake yi ba tare da ya riya cewa ibada ba ce hana shi ko bidi'antar da aikinsa yana da wuya, kamar yadda Ibnu Uthaimin ya yi nuni zuwa haka a fatawar da aka yi masa.

Saidai duk da haka ya kamata kar Musulmi ya zamar da shi al-adarsa kowace juma'a, don kar wasu su fahimci ibada ne.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)