Hukunci Kashe Kwadi Da Cin Namansu!
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum Malam menene ingancin hadisin da yake cewa: "Annabi SAW ya hana kashe Kwadi saboda kukansu Tasbihi ne ga Allah"?
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam, Tabbas ya tabbata a hadisin Abu-dawud mai lambata: (5269) da kuma Nas'i (2/202) cewa: wani likita ya tambayi Manzon Allah akan kashe kwadi saboda sanyawa a magani sai Annabi ya hana shi kashe su". Baihaki ya rawaito daga maganar Abdullahi Bn Amri bn Al-Ass cewa "Kada Ku kashe kwadi saboda kukansu tasbihi ne ga Ubangijinsu". Duk da cewa hadisin zai iya daukar cewa ya ji ne daga Manzon Allah saidai Hafiz Bn Hajar yana cewa " Abdullahi bn Amr bn Ass ya shahara da yin riwaya daga malaman Yahudu da Nasara don haka ba dole ne ya zama daga Annabi SAW ya ji ba. Kashe kwadi haramun ne saboda hadisin Abu-dawud da Nasa'i da ya gabata, kamar yadda cin su ma haramun ne, saboda ba zai yiwu a ci dabba ba sai bayan ranta ya fita. Allah ne mafi sani
Amsawa
✍🏻 DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
_Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana._