HUKUNCIN KOYAN ILIMIN TAURARI (Astrology)
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum Dr. dafatan anwuni lafiya, Allah yasa haka amin.
Akwai wani abu mai kama da ilimi kuma kamar tsafi ta wani fuskar. A turanche ana kiran sa Astrology, har akwai Makarantu da ake karantar da course din a Jami'a, kama daga degree, masters har P.h.d, wasu kuma suna sana'a dashi a kasashen waje, ta bangaren bada shawarwari.
Abin ya dogara ne da sanin taurari, juyawar duniya, rabe raben ruhi da sauransu. Sun raba ruhin Dan Adam gida hudu, akwai; Ruwa, Kasa, Iska da kuma Wuta.
Ko wane ruhi yana tare da wasu taurari wadanda ake ganesu ta hanyar sanin ranar haihuwar mutum. Masu irin wadannan ilimin suna iya fadan halin mutum, kuma a mafi yawanchin lokuta yana zama daidai. Suna bada shawarwari gameda abinda mutum zaiyi, har suna fadawa mutum chewa lura da taurari ko makamanchin haka, yanada sa'a a wuri kaza, ko kuma bashida sa'a. Suna fadan chewa wane yanada taurarin nasara ko kuma wani abu mai kama da haka.
Ina bibiyar abin a mafi yawanchin lokuta, har nafara fahimtan wasu abubuwa gameda hakan.
Minene matsayin sharia
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam, To dan'uwa yin irin wannan nau'i na ilimin taurari haramun ne yana kuma iya kaiwa zuwa ga shirka, saboda Camfi ne da kuma da'awar sanin Gaibu, wanda Allah ya kebanta da shi.
Imamu Katadah yana cewa: "Allah ya halicci taurari ne saboda abubuwa guda uku kawai:
*1.* Gane hanya, kamar yadda Allah ya fada a suratu Annahl aya ta(16)
وعلامات وبالنجم هم يهتدون
*2.* Ado ga saman duniya.
*3.* Jifan kangararrun Shaidanu masu sato Ji daga sama, Allah madaukakin sarki yana cewa a suratul mulki aya ta (5)
ولقد زينا السماء الدنيا Ø¨Ù…ØµØ§Ø¨ÙŠØ ÙˆØ¬Ø¹Ù„Ù†Ø§Ù‡Ø§ رجوما للشياطين.
Yin amfani da Taurari wajan gane Nasara ko rashinta harka ce ta Bokaye, kuma Allah bai tanade su don yin hakan ba, yana kuma kaiwa zuwa hallaka.
Ya halatta ayi amfani da ilmin Taurari wajan gane Alkibla da kuma tabbatar da maslahohin addini.
Don neman karin bayani duba Alkaulu al-mufid 2/102 da kuma Al-mulakkas fi-sharhi kitabittauhid (236)
Allah ne mafi sani
*Amsawa
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
_Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana._