HUKUNCIN MATAR AUREN DA AKAI MATA FYADE

HUKUNCIN MATAR AUREN DA AKAI MATA FYADE 




 TAMBAYA TA 2869
***************
Assalamu alaikum warahmatullah.

Dan Allah malam inada tanbayoyi ne guda uku duk da cewa ta farkon kusan ahade suke.
Tanbaya ta itace 
matar aure ce akai mata fyade sannan taci gaba da kwanciyar aure da mijinta. Shin akwai aure a tsakanin su ko babu?
 kuma zasu iya cigaba da zaman aurensu akan haka?
Sannan zata iya fada masa ko Kuma a'a, saboda gudun zargi ? 

Na biyu Kuma sai ciki ya bayyana atare da ita Kuma sannan taci gaba da kwanciyar aure da mijinta shin akwai aure a tsakaninsu ko babu? kuma meye matsayin auren ? 

Na uku Kuma shine macece a kaima auren dole har Allah yasa ahalin yanzu suna da yara kusan 8 amma tace har yanzu babu digon sonsa a ranta wai zata iyayin karya da wata laluran dan ya saketa wai bazata iya cigaba da rayuwarta dashi ba.

Nagode sosai Allah biyaka da mafificin Alkhairi duniya da lahira amiin ya hayyu ya qayyum.

AMSA
***
Wa alaikis salam wa rahmatullah.

Hukuncin matar da aka yiwa fyade shine: dole ne ta sanar da mijinta saboda hakkinsa na aure. Sannan kuma wajibi ne tayi zaman istibra'i wato domin tabbatar da ko ciki ya shiga ko bai shiga ba. 

Zata zauna tsawon lokacin da zatayi haila. Idan hailarta tazo koda sau É—aya ne, to shikenan ta samu tabbacin cewar ciki bai shigeta awannan fyaden da akayi mata ba. Amma idan har ciki ya shiga, babu damar mijinta ya kwanta da ita sai bayan ta haife abinda ke cikinta. Domin Manzon Allah ï·º ya hana mutum ya shayar da shukar da ba tasa ba. 

Bayan ta haife cikin kuma sai taci gaba da zaman aurenta da mijinta. Domin wannan fyaden bai lalata aurensu ba.

Amma yanzu tunda har taci gaba da mu'amalar auratayya da mijinta, dole wannan abinda ta haifa din ya zamto na mijinta ne. Tunda Manzon Allah ï·º yace "YARO NA SHIMFIDA NE" (wato mamallakin shimfidar shine mamallakin yaron).

Matar da aka yiwa auren dole tana da damar neman yin khul'i da mijinta. Wato ta biyashi sadakinsa shi kuma ya saketa. Amma neman sakin aure ba tare da wani kakkarfan dalili ba, haramun ne. 

Hakanan kuma Manzon Allah ï·º yayi gargadi mai tsanani game da duk matar da taje tayi zina ta samu ciki sannan ta dangantashi zuwa ga mijinta alhali tasan ba 'dansa bane. Yace ba zata dandani komai na rahama ba. Ko kuma Allah bazai dubeta da rahama ba. 

Ya zama wajibi mai wannan tambayar kiji tsoron Allah ki rika tunawa da lahirarki. Duk abinda kika aikata anan duniya fa, zaki tarar da sakamakonsa aranar da babu damar yin Qarya, ko kinyi ma bazata rage miki radadin azaba ba. 

Amatsayinki na matar aure, me ya kaiki har kika kebance da wani Qato, har yayi miki fyade? Kuma in da gaske fyaden akayi miki, me ya hana kiyi eehun sa jama'a zasuji domin su kawo miki 'dauki?? Kuma me yasa baki sanar da mijinki ko danginki don su dauki matakin sanar da hukuma don nema miki hakkin cin zarafin da akayi miki ba?? 

Ki tuba ki nemi yafewar Allah da yafewar mijinki domin hakika kin zalunci kanki kuma kin zalunci mijinki. 

WALLAHU A'ALAM. 

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990


Post a Comment (0)