Ina so a yi min ƙarin bayani akan farillan sallah da sunnoninta da kuma abubuwan da ke ɓata sallah



Tambaya
:
Ina so a yi min ƙarin bayani akan farillan sallah da sunnoninta da kuma abubuwan da ke ɓata sallah
:
Amsa
:
To su dai farillan sallah sun kasu ne gida-2, akwai sharuɗɗan sallah sannan kuma akwai rukunan sallah:
:
Kuma akwai bamanci tsakanin sharaɗi da kuma rukuni. Sharaɗi a na samunsa ne kafin a shiga cikin ibada, shi kuma rukuni a na samunsa ne a cikin ita ibadar kanta. Kuma dole sai kowanne yasamu sannan ibada ta ke cika.
:
SHARUƊƊAN SALLAH (8)
:
1-Balaga
2-Hankali
3-Muslunci
4-Tsarkin kari
5-Tsarkin dauɗa
6-Suturce al'aura
7-Shigowar lokaci
8-Fuskantar alƙibla
:
Kuma gaba ɗayan Malamai sunyi ijma'i akansu. Sai dai Malamai sunyi saɓani akan cewa shin ƙulla niyya da kuma kabbarar harama suma sharaɗi ne ko kuma ba sharaɗi ba ne?:
:
RUKUNAN SALLAH (4)
:
1-Ruku'i
2-Sujjada
3-Tsayuwa
4-Zaman ƙarshe
:
Wannan ma gaba ɗayan Malamai sunyi ijma'i a kansu. Sai dai Mazhabin Shafi'iyya sun ƙara da waɗansu abubuwa kamar haka:
:
1-Sallama
2-Tahiyar ƙarshe,
3-Daidaituwa a cikin ruku'i
4-Salati ga Annabi(ﷺ)
5-Zaman da akeyi tsakanin sujjada
:
FARILLAN SALLAH 15
:
1-Niyya
2-Ruku'i
3-Sujjada
4-Sallama
5-Nutsuwa
6-Daidaituwa
7-Karatun fatiha
8-Tsayuwa dominsa
9-Kabbarar harama
10-Tsayuwa dominta
11-Ɗagowa daga Ruku'i
12-Ɗagowa daga Sujjada
13-Jeranta tsakanin farillai
14-Ƙulla niyyar koyi da liman
15-Zaman ƙarshe wanda za ayi sallama a cikinsa
:
SUNNONIN SALLAH,8
:
1-Karatun sura
2-Ɓoye karatu
3-Bayyana karatu
4-Zaman tahiya na farko
5-Sami'Allahu liman hamidahu
6-Ƙarin addu'a a zaman tahiya na 2
7-Kowacce kabbara in banda ta farko
8-Sanya sutura a gaban mai sallah
:
Sai dai kuma Malamai sunyi saɓani dangane da zaman tahiya, akwai Malaman da sukace zaman tahiya dukkansa farilla ne, to amma mafi rinjayen Malamai sun tafi ne akan cewa zaman tahiya na farko sunna ne, amma zama na biyu farillah ne.
:
ABUBUWAN DA KE ƁATA SALLAH 11
:
1-Rashin yin ƙulla niyya
2-Warwarewar alwala
3-Yin dariya a cikin sallah
4-Wasa mai yawa a cikin sallah
5-Barin wata farilla da gangan
6-Cin wani abu ko shansa
7-Yin magana da gangan wacce ba ta shafi sallah ba
8-Bayyana tsiraici dagangan
9-Yin amai da gangan
10-Juyawa alƙibla baya da gangan
11-Karin raka'a ko sujjada dagangan
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/

3 Comments

Post a Comment