MENENE SHARUDDAN HADA SALLAH?

Assalamu alaikum
Malam ni tambaya ta itace: shin menene sharuddan hada sallah da akeyi(misali magrib da issha) sannan kuma idan za a hada ana sake wani kiran sallar ne daban ko ta magrib ta wadatar?

Saboda naga wasu suna sake kiran sallar,  wasu kuma basa sakewa, wasu kuma suna sakewa amma se an kashe speaker sannan kuma a hankali ladanin yake kira...shin ya abin yake?

Allah shi qara ilimi...
AMSA : Wa'alaikumussalam!
1-Sharudan hada sallah;sai ya zamanto cewa akwae wani karfaffen Dalili wanda zaia hana haduwar mutane a jam'i, missali ( Hadari wanda ake tsammanin ruwa zai iya sauka, Hanya mara kyau da chabali, iska mai karfi, tsananin duhu, tsoron wani abu da zai iya sauka  da dai sauran su. 
2-kiran sallah dai ya tabbata daga manzan Allah anayi yayin ko wacce sallah ta farilla. Har manzan Allah saw Yace ko da mutum shi kadai ne a daji ya kira sallah Saboda falalar dake ciki.amma zance mafi rinjaye wanda ya tabbata a sunnah shine;ba sai an sake Kiran sallah ba, dalili (manzan Allah saw ya hade sallar mgrib da isha'i a musdalifa tare da Kiran sallah daya iqama biyu) Kiran sallar magriba da kuma iqama a kowacce.malikiyya sunzo da cewa za'a kara Kiran sallah Amma a Cikin masallaci ba a waje ba.amma manzan Allah saw ya kasance
yana hade sallolin magriba da isha'i da Kiran sallah daya iqama biyu. Allah ne mafi sani.
  
   ✍Zauren Sunnah Group.Mata da Maza (07069683528 )✍

4 Comments

  1. Allah yasaka da alheri toh mallam idan kuma anriga da anfara sallahfa ba tareda iqama ba menene hukunci yenke sallah?

    ReplyDelete
  2. Yayyafi ya na sa ahada magriba da i sha i

    ReplyDelete
Post a Comment