IDAN MACE TA YI BARI BAYAN MUTUWAR MIJINTA DA WATA HUDU, TA KAMMALA IDDARTA

IDAN MACE TA YI BARI BAYAN MUTUWAR MIJINTA DA WATA HUDU, TA KAMMALA IDDARTA



*TAMBAYA*❓
:
Salam alaikum malam mace ce mijinta ya rasu tana da cikin wata hudu sai tayi bari bayan rasuwar mijin da kwana 3 yaya takaba din ta zai kasance?
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikum assalam wa rahmatullhi
Mutukar cikin ya kai wata hudu, to ta kammala iddarta .

A cikin suratul Dhalak aya ta (4), Allah ya bayyana cewa: iddar mace Mai ciki tana kasancewa idan ta haife cikinta.

Duk lokacin da ciki ya kai wata hudu, dukkan hukunce-hukuncen haihuwa suna hawa kansa, a zancen da ya fi inganci. Hadisin Abdullahi Dan Mas'ud ya tabbatar da cewa ana busawa yaro rai idan ya cika kwana (120) a cikin mahaifiyarsa.

*Allah ne Mafi sani.*

✍️Amsawa: *Dr Jamilu Yusuf Zarewa*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)